Daga Ibrahim Muhammad
Hajiya Amina Muhammad Babandede, yaya ga sabon Magajin Rafin Haɗejia da aka naɗa, ta bayyana naɗin da aka yi wa ƙaninta da cewa abin farin ciki ne ga zuriyarsu bisa tabbatar musu da wannan sarauta da suka gada.
Ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da ‘yan jarida ta yi nuni da cewa tunda aka sanar musu an ba su wannan sarautar har an bayar da takarda suke ta dokin jiran ranar naɗin kullum tambaya suke yaushe ne? Ga shi Allah kawo lokacin ya nuna musu suna godiya ga Allah bisa wannan rana.
Hajiya Amina Muhammad Babandede ta ce su tsakaninsu da jama’a da yin hidima gare su abu ne da suka gada tun daga Madaki Ahmadu zuwa Madaki Sarkiki zuwa Muhammadu Babandede Sarkiki har zuwa kan shi da aka naɗa, kamar yadda mahaifinsu yake yana kwatanta hidima ga al’umma, shi ma suna addu’ar Allah ya ƙara taimakonsu a kan abin da ake a ƙara cigaba.
Ta ƙara da cewa babu abin da za su ce wa Sarkin Haɗejia, domin abin da ya yi musu na tabbatar da sarautar Magajin Rafi a gidansu, sai dai su yi masa addu’a tun daga kan mahaifinsa har zuwa kansa da ma wata alaƙa ce ƙullalliya tsakanin mahaifinsu da mahaifinsa, har kuma ta zo da shi da babban wansu babban Kwanturolan na hukumar shige da fice mai ritaya Babandede saboda haka suna addu’a ga Sarki. Yadda suke yi wa iyayensu haka shima suke saka shi a ciki.