Tue. Apr 1st, 2025

Mun Ji Daɗin Muƙamin Da Gwamnan Kano Ya Bai Wa Sani Danja -Bargaja

By Saleh Aliyu Jan 7, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban Gidauniyar haɗin kan Hausawan duniya reshen Nijeriya, Talban Isah, Alhaji Shiru Adamu Bargaja ya yaba wa Gwamnan jihar Kano bisa naɗa shugaban Gidauniyar reshen jihar Kano, Alhaji Sani Musa Danja a matsayin mai ba shi shawara a kan matasa.

Ya ce wannnan matsayi da aka bai wa Sani Danja an yi bisa cancanta domin dama shi mutum ne na matasa da ya daɗe yana bayar da gudunmawa ga cigaban matasa a ɓangarori da dama.

Alhaji Shitu Adam Bargaja, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar Sakkwatawa da Zamfarawa da Kabawa mazauna jihar Kano da Jigawa ya ce, wannan matsayi da aka bai wa Musa Danja karramawa ce a gare su da gidauniyar su ta haɗin kan Hausawan duniya ƙarƙashin shugabansu na duniya Muhammad Sa’idu Ghana.

Alhaji Shitu Adamu Bargaja ya yaba da irin ɗimbin ayyuka da Gwamna Abba Kabir Yusuf yake musamman na gina cigaban matasa, kuma suna da yaƙinin naɗa Sani Musa Danja a matsayin mai ba shi shawara a kan matasa da cewa zai taimaka masa sosai wajen cimma manufofinsa.

Alhaji Shitu Adam Bargaja ya ce, “A madadin dukkan ‘yan Gidauniyar na Hausawa da haɗin kan Hausawa na duniya reshen Nijeriya muna yi wa Sani Danja addu’a da fatan zama jakada na gari a gare mu da al’ummar Kano wajen ci gaba da hidimtawa al’umma kamar yadda ya saba,”.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *