Tue. Apr 1st, 2025

Ministan Sufuri Ya Yaba Wa Izala Kan Shirya Musabakar Ƙur’ani

By Saleh Aliyu Jan 5, 2025

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ministan Sufuri, Sanata Ahmed Alƙali ya yaba wa ƙungiyar Izala ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sheikh Sani Yahaya Jingir bisa jajircewa wajen shirya aikin alkhari na ilimi da ilmantar wa musamman a kan abin da ya fi komai muhimmanci a harkar ilimi wato ilimi a kan Ƙur’ani.

Ministan ya yi wannan bayani ne ta bakin babban mataimakansa Farfesa Shu’aibu Abdullahi Ɗan’wanka a wajen rufe musabaƙar Ƙur’ani da ƙungiyar ta gudanar a Kano na tsawon mako daya.

Ya ƙara da yi wa ƙungiyar da shugabannin ta da masu hidimta ta mata fatan alkhari. Ya jinjina musu da yaba wa ƙwazon dukkan ‘yan takara da suka shiga musabaƙar da suka fito daga jihohin ƙasar nan har ma da na jamhuriyar Nijar da Ghana.

Ministan ya ƙara da cewa a shirye yake ya ci gaba da ba da gudunmuwa a duk wani abu da ya taso a ƙungiyar domin bunƙasa koyarwar addinin Musulunci.

Ministan Sufurin ya gode wa ƙungiyar ta Izala bisa ƙaranci da girmamawa da aka yi masa na gayyatarsa taro na alkhairi na musabaƙar Ƙur’ani na ƙasa kashi na 28 a jihar Kano wanda hakan babban karamci ne a gare shi .

Farfesa Shu’aibu Abdallah Ɗan’wanka ya ba da haƙuri a madadin Ministan na Sufuri kasancewar ba shi ne ya zo da kansa ba sai wakilci saboda wasu dalilai na aiki da suka taso masa.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *