Daga Ibrahim Muhammad
Ɗalibai daga Jami’ar Bayero Kano sun ziyarci Mataimakin Sifetan ‘yan sanda mai kula da Shiyya ta ɗaya.
Ɗaliban, waɗanda suka fito daga Tsangayar fannin shari’a na Jami’ar Bayero, sun kai ziyarar ne domin ƙulla kyakyawar alaƙa kasancewar ‘yan sanda sune kan gaba wajen tabbatar da bin doka da dda da kuma bincike.
A cewar Barrister A’isha, wadda ta jagoranci ɗaliban guda 50 ta ce, sun gamsu da yadda Shiyya Ta Ɗaya ke gudanar da aikinta na tabbatar da tsaro da kare rayuka al’umma.
AIG Ahmed Ammani Manumfashi, wanda ya yi magana da yawun rundunar, ya yaba wa ɗaliban, tare da jan hankalinsu wajen ƙara ƙaimi a kan abin da suka sanya a faba
Wasu sassa na rundunar da suka haɗa da sashen shari’a da bincike sun yi wa ɗaliban bita game da ayyukan su.