Tue. Apr 1st, 2025

Matatar Fatakwal Ta Fara Gwajin Tace Danyen Man Fetur

By Gazali Haruna Jan 2, 2024 #fetur #mai

Matatar man Najeriya da ke birnin Fatakwal ta fara aikin da jami’ai suka ce na gwaji ne, bayan da ta fara tace danyan man da kamfanin kula da albarkatun man kasar na NNPCL ya fara bata.

Bayanai daga wasu majiyoyi sun ce ana sa ran nan ba da jimawa ba, matatar man ta Fatakwal za ta fara samar da tataccen man fetur da sauran albarakatunsa ciki har da man diesel, ga wasu jihohin Najeriya akalla 12.

A ranar 21 ga watan Disambar da ya gabata, gwamnatin Najeriya ta sanar da kammala aikin gyaran matatar da ke jihar Rivers, wadda ta ce za ta rika tace danyane man da yawansa zai kai ganga dubu 60 a kullum, da zarar an kammala hutun bikin Kirsimeti.

Ana dai sa ran da zarar matatar man ta Fatakwal ta fara aiki a samu saukin farashin man fetur a jihohin da za su fara samunsa, kodayake kwararru sun dade da bayanin cewar saukin farashin ba zai kai yadda akasarin mutane ke zato ba, har sai sauran matatun man gwamnatin Najeriyar da ke Warri da Kaduna sun fara aiki.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *