Mon. Mar 31st, 2025

Matasan PDP Na Arewa Sun Amince Da Shugabancin Damagun

By Saleh Aliyu Oct 22, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Matasan PDP na jihohi 19 na Arewacin Nijeriya sun jaddada goyon bayansu ga shugaban jam’iyyar PDP Iliya Umar Damagun. Wannan na ƙunshe na cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai mai ɗauke da sa hannun Hon. Biniya Yahuza Gabari.

Sanarwar ta ce suna goyon bayan shugabancin riƙo da Iliyasu Umar Damagun yake ne bisa la’akari da irin matakai da yake ɗauka na haɗa kan jam’iyyar da kawo mata karɓuwa da cigaba.

Sun nuna cewa sun gamsu da matakin da gwamnonin jam’iyyar PDP suka zartar na nuna goyon baya ga cigaba da jagorancin jam’iyyar PDP da Damagun yake wannan tunani ne mai kyau da zai ƙarfafa cigaban jam’iyyar a ƙasar nan.

Matasan na PDP na jihohi 19 na Arewa sun bayyana cewa yawanci masu ƙoƙarin ƙalubalantar shugabancin na Iliya Umar Damagun ba masu son cigaban jam’iyyar bane suna fakewa ne da jam’iyyar suna haɗa fitintinu domin cimma wata bayayyiyar manufa tasu ta son rai.

Hon. Biniya Yahuza Gabari ya yi kira ga duk ɗan PDP mai kishinta da don cigaban ta ya bai wa jagorancin Damagun goyon baya domin jam’iyyar ta samu nasara a 2027 ta kawar da APC daga mulkin ta da ya jawo ƙuntata wa al’ummar ƙasar nan ta sa su a mawuyacin halin ƙuncin rayuwa da ba a taɓa gani ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *