Thu. Apr 3rd, 2025

Matasan Arewa Na APC Sun Yaba Wa Tinubu Kan Sakin Yaran Da Ake Tsare Da Su

By Saleh Aliyu Nov 7, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

APC Arewa Youths Merger Group ta yaba wa shugaban ƙasa Ahmad Bola Tunubu bisa kaɓar ƙorafinsu da kira da suka yi masa a kan ya sa a saki yara da aka tsare a kan zanga-zanga cikin awa 48.

A cikin wata takardar sanarwa da ke ɗauke da sa hannun jagoran matasa na APC Arewa Merger Group, Hon Musa Mujahid Zantawa aka raba wa manema labarai ya ce, sun yi matuƙar jin daɗi da farin ciki da yafewa yaran da shugaban ƙasa ya yi bayan amsa kira da suka yi masa, ya kuma miƙa su hannun gwamnonin jihohinsu wanda da ma haƙƙinsu ne su yi ƙoƙarin karɓo su, amma suka kasa aiwatar da hakan.

Ya yi nuni da cewa musamman ma Gwamnan jihar Kano da mafi yawan yaran ‘yan asalin Kano ne, kuma shi ne ma ya bai wa Kwamishinan Shari’a na jihar umurnin a kai yaran kotu a hukunta su, amma ake nema a sa siyasa a maganar. “Dole ne yanzu gwamnatin Kano ta fito ta nemi gafarar waɗannan yara da a dalilin matakin da ta ɗauka ne suka shiga wannan yanayi,” in ji sanarwar.

Ƙingiyar ta ce a lokacin da suka kai wa yaran ziyara a inda ake tsare da su sun kai musu tallafi na kayan abinci da na buƙatun yau da kullum. Sun yi musu alƙawari dama a cikin awanni 48 za su nemi alfarma wajen shugaban ƙasa ya sa a sake su, kuma sun nema, shugaban ƙasa ya amsa kiran nasu ya sa aka sake su.

Hon. Musa Mujahid Zantawa ya ƙara jaddada godiya ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunubu a madadin matasan APC a kan wannan shawara tasu da ya ɗauka hakan ya tabbatar da cewa shi ɗan damakwaraɗiyya ne. Sannan suna ƙara kira a gare shi ya ɗauki nauyin karatun waɗannan yara da aka saki domin su zama masu kyakkyawar makoma nan gaba idan suka zama masu ilimi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *