Thu. Apr 3rd, 2025

Matasa Masu Tasowa Su Daure Su Aikata Alkhairi -Baban Hajiya

By Saleh Aliyu Feb 15, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Ɗaya daga manyan baki a taron na ƙaddamar da littafin Hajiya Malama ‘Yar Kyakke Ɗanbatta, Alhaji Idris Ahmad Baban Hajiya ɗan asalin Ɗanbatta da yake kasuwanci garin Daura ya yi nuni da cewa harkar hidima ta addini tana da nauyi da wahalar yi matuƙa, don haka matasa masu tasowa su daure wajen yaƙi da shaiɗan ta yin abubuwa na alkhairi saboda wannan shi ne idan ka kashe kuɗin ka za ka ji daɗi da natsuwa fiye da komai.

Baban Hajiya ya ce ya ji daɗi kan wannan littafi yana kuma ta ya ta murna su ma suna fata Allah ya ba su iko wata rana da za su aikata wani abu na alkhairi da za a riƙa tunawa da su ya kuma roƙi Allah ya yi mata rahama domin a lokacin fa ta yi wannan ƙoƙari ba a samun maza masu ilimi sosai, amma Allah ya taimake ta a matsinta ta mace Allah ya aura mata rana ta yi kuma suna kyakkyawan fata Allah ya albarkaci bayanta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *