Daga Ibrahim Muhammad Kano
Ma’aikata da masu kamfanoni a rukunin ƙananan masana’antu na Dakata da ke jihar Kano sun nuna damuwa da kuma ɗora zargi a kan kamfanin rarraba wuta hasken wutar lantarki na KEDCO da neman kassara musu sana’o’i ta hanyar ƙin ba su wuta da ya kamata da hakan yake jawo musu ɗimbin asarar da rasa aikin yi a tsakanin matasa.
Wannan ta sa ma’aikata a rukunin ƙananan masana’antun na Dakata suka ɗauki mataki suka soma gudanar da Sallah da yin addu’o’i domin neman Ubangiji ya yi musu maganin duk wanda yake da hannu a ƙoƙarin kassara sana’ar tasu da hakan ke sanadin durkusar da aikin da suke yi.
An soma gudanar da taron addu’ar a rukunin ƙananan masana’antu a safiyar Laraba ya sami halartar daruruwan leburori da masu masana’antu da suka nuna rashin jin daɗi bisa rashin ba su wuta da neman ɗauki daga duk masu ruwa da tsaki domin dafa musu wajen samun mafita daga wannan matsala da suke ganin da gangan ake nema a jefa su
Surajo Musa ɗaya daga cikin shugabanni a ɗaya daga rukunin masana’ntun na Dakata ya ce sun shiga wani yanayi mai wuya sakamakon rashin wuta da suke fama da shi a ƙananan masana’antun sun doshi sama da kwanaki 90 ba cikakkiyar wuta da hakan ya jawo musu koma-baya sosai sakamakon mutane da yawa a nan suke samun na abinci ga yanayin matsanancin rayuwa da ake a ciki.
Ya ƙara da cewa mutane masu sarrafa kayayyaki da yawa sakamakon rashin wutar da za su yi aiki an shiga mummunan yanayi, wasu ma sun zama kamar sun zautu, wasu sun shiga wani yanayi har suna taɓa kayan wani, wanda ma ba ya maula ya shiga yi.
Ya yi nuni da cewa bayan an sami matsala ta wuta da ta shafi Arewa a kwanakin baya an dawo ana samar da wutar ta hanyar Jos ake bai wa masana’antu, amma sai KEDCO suka ware wasu masana’antu suke ba su suke hana ƙananan masana’antun Dakata, sun nemi dalili da ya sa ake hana su wutar sai aka ce musu wutar tana bata ne, amma bayan sun gudanar da bincike da kansu, Manajan Darakta na KEDCO ya tabbatar musu ba a bangaren su masu ƙananan masana’antu na Dakata take ɓata ba, sun gano inda take salwanta.
Ya ce amma duk da haka sai aka ya yi musu kuɗin goro baki ɗaya, sun kuma turza a dawo musu da wutar, amma aiki har sun nemi ɗaukin shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da Kwamishinan kasuwanci sun zauna da Manajan Daraktan na KEDCO, amma ba ya ba su wutar yadda ya kamata sai ta awa biyu kaɗai da ba za ta isa su yi aiki ba, sannan kuma su caje su kuɗin wuta mai yawa ta ɗora su a tsarin ‘Band A’.
Surajo Musa ya ce yanzu har ta kai ga masu jari sun cinye, ƙananan leburori babu aiki, ita kuma gwamnati da suke taimaka mata wajen samar da aiki ga ɗimbin al’umma ta kau da kai daga gare su, an ƙyale su a halin da ba su taɓa tsintar kansu ba na tasku.
Shi ma Alhaji Murtala Isa Sadauki mai kamfanin mai da roba a rukunin ƙananan masana’antu na Dakata ya ce, leburorin sune suka shirya taro na addu’ar Alaƙunutu saboda suna ganin da su fito su yi zanga-zanga sai suka zaɓi su shirya addu’o’i domin sun ga yadda masu masana’antu suke riƙe da su da kima da daraja suka samar musu da aiki sun tabbatar ba su da laifi wajen rashin yin aiki.
Ya ce suna zargin mutum ɗaya ne a kamfanin KEDCO Abubakar Yusuf, wanda shi ne Manajan Daraktan yake neman saka dubban leburori cikin tasku. Suna zargin sa ne saboda sun za ci aiki yake da ya kamata sun ba shi duk wani goyon baya a ƙungiyarsu ta ƙananan masana’antu na Dakata sun taɓa gayyato shi su zauna da shi domin su fahimci juna, amma ya ƙi zuwa suka nemi ya ba su dama su same shi bai yarda ba, har sai da suka sami shugaban KEDCO maji dadin Gumel, sannan ya ba shi umurni ya zauna da su a yayin zaman har sai da suka gayyato shugaban ma’aikata na Kano aka cimma matsaya, amma duk da haka Manajan Daraktan na KEDCO ya ƙi yi musu abin da ya kamata na kunno wutar zaman da suka yi yau kwanaki sama da 15 duk maslaha da za a yi an yi.
Murtala Isa Sadauki da aka fi i sani da Alaramma ya ce, abin lura KEDCO ba ita take da doka ba, doka tana nan a matsayinta na doka ya kamata ya zama me bin ta, idan yana zargin sun yi masa laifi ya kai su hukumar da gwamnati ta tanada na kai ƙorafi, amma bai kai su ba, domin su ma da suka zarge shi da wani laifi a baya can suka kai shi ta yi musu hukunci. “Wannan ya nuna suna zargin yana da wani ra’ayi na son zuciya da wani ƙulli na rusa tattalin arziƙin jihar Kano ke nan,” in ji shi.
Don haka suka taru suka kai kukansu ga Allah za su kuma ci gaba da irin wannan zama na addu’o’i domin Allah shi ne mai maganin duk wata masifa.