Tue. Apr 1st, 2025

Marayu Da Daliban Tsangaya 110 Suka Amfana Da Tallafin Kafilatul Mahabbah A Funtuwa

By Gazali Haruna Jan 21, 2024

Daga Hussaini Yero, Funtua

Cibiyar Kafilatul Mahabba ta Kasa Reshen Karamar Hukumar Funtuwa, Karkashin jagorancin shugaban Cibiyar na Kasa, Farfesa , Ibrahim Makari ta ba Marayu Maza da Mata da Daliban Makarantun tsagaya tallafin kayan sawa dari da goma a Karamin Hukumar Funtuwa cikin Jihar Katsina.

Kodinita na Reshen Funtuwa,Br Ahmad Tijani Magaji ya bayyana cewa, ayyukan kungiyar sun hada da shirya taruruka a wasu mahimman ranaku da muke da su a cikin shekara ,dan haka Ayau ce ranar Yaumul Kiswa,shine mukaga ya dace,mu rayata da tallafin kayan sawa dari da goma ga marayu da Daliban Tsangaya,dan suma amfana da ayyukan wannan cibiya mai albarka a wannan gari namu mai albarka a wannan gari namu .”

” Ahmad Tijani ya kuma kara bayyana ayyukan cibiyar kamar haka,Ziyartar Asibitoci daba Masara lafiya tallafi,ziyara gidan gyara halinka,da Gangamin tsaftace muhalli a karshen kowane wata cibiyar ke aiwatarwa yanzu haka Karamar Hukumar ta Funtuwa.

Malam Yusuf Lawandi ,shugaban Cibiyar Riyadu Salihu da Malam Gazali ne suka gabatar da kasidu akan mahimmancin bada tallafi a addinin Musulunci kuma sun gargadi mawada akan rike abun hannun su ga mabukata wanda wannan yana tauye arziki mawadaci .

Kuma sun Jinjina ma Kafilatul Mahabba wajan taimakon al’umma lallai abunkoyi ne da wannan cibiya a Funtua da kasa baki daya.

Shugaban Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (sea) na Funtuwa, Muhammad Busiri da ya samu wakilin ma’ajin kungiyar,Alhaji Bashir Yero,ya bayyana cewa,wannan cibiya tazo daidai loakcin da ya dace,dan yanzu lokacin ne da alumma suke cikin matsi na rayuwa da suke bukatar tallafi,muna Jinjina da godiya ga iyayan wannan cibiya ta Kasa da suka akawo abun arziki a cikin mu,Allah ya albarkaci wannan cibiya ya sanya kudirinta ya cika na tallafawa alumma amin.

Anasa jawabin Sakataren Cibiya na Karamar Hukumar Funtuwa, Zaharadini Ibrahim,ya bayyana cewa,wannan kungiya tana samun kudin shigane daga mambobinta basu zuwa ko’ina dan neman taimako amma duk wanda ya kawo taimako zamu amsa hannu biyu in sakataren Zaharadini Ibrahim.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *