
Ma’aikatan gwamnati sun zargi gwamnatin shugaba Bola Tinubu da rashin kula da halin da suke ciki saboda gaza biyansu albashi a kan lokaci.
Ma’aikatan ta hanyar kungiyoyinsu sun yi wannan zargin ne kan jinkirin da ake samu na biyan albashi, tagomashi da sauran kudaden alawus-alawus da suka saba samu .
Kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati ta ƙasa, ASCSN, ta bayyana rashin jin dadin ta musamman kan jinkirin biyan albashin ma’aikata na wata-wata.
Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, Tommy-Etim Okon, Shugaban ASCSN ya ce ya kamata gwamnati ta gaggauta biyan albashi da alawus din ma’aikata.
Ya kara da cewa, tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau karagar mulki, ba a biyan albashin ma’aikata a kowane wata da kuma biyan albashin ma’aikata a kan lokaci, wanda hakan ke shafar samar da ayyukan yi da walwala.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta kula da halin da ma’aikata ke ciki, duba da irin halin kuncin da ake ciki a kasar nan.“Kowace rana tsadar rayuwa tana kara hauhawa, ta yaya ma’aikata za su biya kudin mota zuwa ofis, ta yaya tattalin arziki da sauran masana’antu za su tsira, idan ba a samun hada-hadar kudade?“