Tue. Apr 1st, 2025

Lokacin Hamayyar Siyasa Ya Wuce, Ku Zo Mu Gina Zamfara –Gwamna Dauda Lawal

Wannan ita ce cikakkiyar hirar da kafar yada labarai ta BBC Hausa ta yi da gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal dangane da nasarar da ya samu a kotun koli kan zabensa da ma wasu tambayoyi.

DAUDA LAWAL: ina yi ma Allah godiya mai kowa mai komai da ya kawo mu wannan rana da kotun koli ko wanda ake ce ma kotun Allah ya isa ta yanke hukunci wanda shi ne na karshe a kan maganar gwamna na jihar Zamfara. Kuma Alkalai sun yi abin da yakamata. Abu ne wanda gaskiya ni dama ban taba shakka cewa haka ba zai faru ba tun farko. Alhamdulillah!

Ko da ake wannan shari’a wallahi billahi hankalina bai taba tashi ba don na san cewa ba ka canza hukuncin Ubangiji. Abu ne wanda yake mun san cewa mun yi shi a kan gaskiya.

BBC Hausa: wanne mataki za ka dauka a kan matsalar tsaro?

DAUDA LAWAL: na farko dai abin nan mun zo mun same shi ne ana yin shi fiye da shekara goma. Abu ne wanda da muka zo muka ce za mu yi bakin kokarinmu da ikon Allah za mu kawo ma al’umma sauki. Kuma tunda na amshi mulkin nan a kai muke. Muna nan muna yaki da ‘yan ta’adda. Muna yaki da ‘yan bindiga kuma alhamdulillahi muna samun nasarori daban-daban.

BBC Hausa: akwai fahimta tsakaninka da gwamnatin Tarayya kan tsaro?

DAUDA LAWAL: muna da kyakkyawan fahimta tsakanina da gwamnatin tarayya. Abu ne wanda ka sani cewa maganar tsaro gwamna ku san ba abin da zai iya yi; sabonda gwamna bai da sojoji, gwamna bai da ‘yan sanda, da makamantansu, saboda haka dole ne sai mun samu hadin kai daga gwamnatin tarayya. Kuma dukkansu sun yi alkawari a kan cewa za su ba mu goyon baya kuma alhamdulillahi muna samun wannan goyon baya daga gwamnatin tarayya. Fatanmu shi ne su ci gaba da ba mu wannan goyon baya har mu kai karshen wannan bala’i da muke fama da shi.

BBC Hausa: ko kun zauna da karamin ministan tsaro?

DAUDA LAWAL: ba mu zauna da shi ba. Amma ban ce kuma ba zan zauna da shi ba.

BBC Hausa: da gaske ne cewa ya kira ka ba ka dauki wayarsa ba?

DAUDA LAWAL: wannan ba gaskiya bane ba. Domin ni ban taba ganin ya kira ni ba. Watakila wata lambar yake kira ba tawa ba. Amma ya san lambata, kuma nima ina da lambarsa.

BBC Hausa: ka taba gwada kiransa?

DAUDA LAWAL: a gaskiya ban taba buga mishi waya ba, kuma shima bai taba buga min ba. Yanzu lokacin siyasa ya wuce, lokacin hamayya ya wuce. Duk wani wanda yake da kishin al’ummar jihar Zamfara, yana son ci gaban al’ummar jihar Zamfara, to ya zo mu hada karfi da karfe mu taimaki al’umma mu gina Zamfara. Ba maganar ‘party’ bane ba, duk wani wanda yake dan Zamfara wallahi a shirye nake da na zauna da shi in dai zai kawo ci gaban al’ummar jihar Zamfara.

BBC Hausa: me jama’ar Zamfara za su gani a gwamnatinka?

DAUDA LAWAL: ina godiya ga al’ummar jihar Zamfara, saboda tun farkon tafiyarnan sun nuna min so da kauna. Tsaro muna nan muna bakin kokarinmu. Na biyu; idan ka duba harkar ilimi. Na daya; mun biya da duk wani dan makaranta da yake bai amshi satifiket dinshi ba. Na biyu yanzu mun bayar da ayyuka a kananan hukumomi goma sha hudu (14) a kowacce makaranta ta Firamare da Sakandare da gyare-gyaren da za a yi musu. Cikin wancan sati, mun raba taki, mun raba iri, mun raba magunguna, mun raba mashin-mashin na noma wanda za su inganta noma wanda har yanzu a kai muke; wannan na noman rani ne ba wai na damina ba.

By admin

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *