Tue. Apr 1st, 2025

Lauyoyi Sun Shirya Taron Bita Kan Hulɗa Da Masu Almundahanan Kuɗaɗe A Kano

By Saleh Aliyu Feb 27, 2025

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa reshen Ungogo ta jihar Kano, ta gudanar da taron ƙara wa juna sani na yini ɗaya na horar da ƙwararru kan ɗa’a da kuma yaƙi da safarar kuɗaɗen almundahana.

A jawabinsa a yayin taron, Antoni-janar kuma Kwamishinan Shari’a na jihar Kano, Barista Haruna Isah Dederi, wanda mataimakin Darakta a Ma’aikatar Shari’a, Shamsi Abdullahi ya wakilta, ya yi kira ga dukkan lauyoyi su haɗa hannu su bai wa ƙungiyar lauyoyi musamman ta Ungogo haɗin kai a ƙoƙarinsu na yaƙi da almundahana.

Ya ƙara da yin kira a kan lauyoyin su tsaya su yi abin da ya kamata kada su riƙa abin da ba daidai ba, su zama masu gaskiya da riƙon amana kada su yarda gurɓatttaun mutane su riƙa amfani da su wajen cutar da al’umma da ɓata wa kansu suna.

Barista Haruna Isah Dederi ya yaba wa reshen Ungogo na ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa, musamman shugabanninta ƙarƙashin Barista AA Gwadabe sun yi ƙoƙari sosai wajen shirya irin wannan muhimmin taron ƙara wa juna sani ga lauyoyi za ta yi amfani sosai duba da yadda ƙalubale iri-iri na rayuwa ke tasowa ana samun wasu lauyoyi na kaucewa daga kan hanya suna faɗawa cikin tarkon marasa gaskiya.

Sannan ya nemi lauyoyi da sauran mahalarta su yi kyakkyawan amfani da abin da suka koya.

Tun da farko a jawabinsa shugaban ƙungiyar lauyoyi na ƙasa reshen Ungogo, Bsristss Ahmad Abubakar Gwadabe ya ce wani umurni ne daga uwar ƙungiyarsu ta ƙasa ta bayar bayan bita da aka shirya wa dukkan shugabannin ƙungiyoyin lauyoyi na jihohi na ƙasa baki ɗaya, kuma aka zartar kowa ya dawo reshensa ya faɗakar da mambobinsu a kan aikinsu da kuma maganar mu’amalar fitar da kuɗi fiye da kima da doka ta tanada, shi ya sa suka gayyato ‘yan ƙungiya da sauran mutane domin su fa’idantu da wannan bita daga manyan masana da suke aikin shari’a da jami’an tsaro da masu yaƙi da kuɗin haram.

Shugaban na ƙungiyar lauyoyi na jihar Kano, Ahmad Abubakar Gwadabe reshen Ungogo ya ce ita doka tana aiki a kan kowashi Lauya idan ya wuce iyakarsa ta halatta kuɗin haram ko ba da kariya ga ta’addanci akwai mataki na doka a kansa don haka sun shirya bitar ne don faɗakar da ‘yan’uwansu da ƙa’idoji idan mutum zai ɗauke su aiki su, sun san wacce mu’amala yake gudanarwa domin su gujewa hulɗa da baragurbi da zai jefa su a abin da ba su ji ba, ba su gani ba.

Barista A. A. Gwadabe ya ce abin da suke so su cimma shi ne faɗakar da lauyoyi da ba su daɗe da fara aikin ba, domin su san aikinsu da nauyin da yake a kansa na waɗanda suka ɗauke su aiki da kuma abokan mu’amalarsu, wane nauyi ne da haƙƙi ne, wanda ya kamata a riƙa kulawa da su ,domin a sami tsafta a wajen kyautatuwar aikin.

A jawabinsa, ɗaya daga cikin jami’an ROLAC a jihar Kano da suka tallafa wajen shirya taron, Isma’il Bello ya ce, wannan na daga tsarin aikinsu na ƙarfafa wa lauyoyi don ganin sun ƙware a aikinsu, musamman kan abin da ya shafi almundahana, shi ya sa suka ba da gudunmuwa domin horar da reshen lauyoyi na Ungogo.

Ya ce tun farko sun gayyaci ƙungiyoyin lauyoyi na reshen Ungogo da na reshen Kano zuwa Abuja aka ba su horo na tsawon kwana biyu a kan yaƙi da kuɗaɗen almundahana su kuma suka dawo zuwa Kano suke horar da mambobinsu. Wannan na daga tsarin ayyukansu na tallafa wa musamman lauyoyi matasa su dage su fahimci sha’anin aikinsu da tsare gaskiya da iya cimma muradunsu yanda yakamata.

Isma’il Bello jami’in na ROLAC ya yi fatan duk wanda ya halarci bitar zai yi ƙoƙari ya yi amfani da abin da ya koya wajen ba da gudunmawa ga cigaban al’umma ta fannin aiki da abin da ya koya.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *