
Jama’a sun yi wa dan majalisa wakilai mai wakiltar mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a jihar Filato Hon. Yusuf Gagdi, caa bayan ya bai wa ‘yarsa kyautar sabuwar motar alfarma kirar Lexus RX Crossover SUV.
Kyautar dai ta biyo bayan kammala karatunta a makarantar Lead British International School da ke Abuja, da kuma yadda ta taka rawar gani a jarrabawar da ta yi ta neman shiga Jami’a (UTME).
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, Aisha Gagdi, ta kammala karatunta ne a ranar Asabar, kuma Saminu Maigoro ne ya wallafa kyautar bikin a dandalin sada zumunta na Facebook, inda aka ga hotunan matashiyar tare da mahaifanta da kuma motar alfarma.
Maigoro ya taya Aisha murna a sakonsa, inda ya ce, “Ina taya A’isha Yusuf Gagdi murnar kammala karatu a makarantar Lead British International School Abuja. Muna fatan ya zama matakin farko na ci gaban rayuwarki. Domin murnar kammala karatun ta da kuma rawar da ta taka a JAMB, mahaifinta ya ba ta mamaki da kyautar mota.”
Rubutun ya haifar da ce-ce-ku-ce daga masu amfani da yanar gizo. Wasu masu amfani da shafukan sada zumunta sun mika sakon taya murna ga A’isha, yayin da wasu ke sukar dan majalisar da rashin kula da halin matsin tattalin arzikin Nijeriya da ake ciki.
Wata mai suna Kimkigo Kimkigo, ta taya A’isha murna, yayin Kamardeen Ibrahim Umar ya bayyana takaicinsa inda ya bayyana rashin jituwar da ke tsakanin ‘yan siyasa da talakawan Nijeriya:
“Ina taya ta murna, amma ta yaya za mu samu ci gaba a kasar nan da wani haziki dan talakan Nijeriya ke ta faman neman kudin biyan JAMB, WAEC. ko NECO, idan ya yi sa’a ya samu ya biya kudin jarabawar kuma ya ci nasara, ba zai iya biyan kudin karatun Jami’a da ke hauhawa kusan kullum ba. Sannan a daya bangaren kuma ‘yan siyasar da talakawan kasar suka zaba mulki sun shagaltu da yi wa Iyalansu kyautar kece raini?” Ya tambaya.
Shi ma Amar Ibrahim ya nuna rashin jin dadinsa: “Dubi yadda talakawa ke kwana da tashi da yunwa, amma su ‘yan siyasa suna facaka da kece raini. Mu ne musabbabin matsalolinmu.”
Shi ma wani Mai sharhi kan al’amuran yau da kullum da ke zaune a kasar Jamus, Dakta Muhsin Ibrahim, ya shawarci ‘yan siyasa ne su guji aikata abin da zai kara fusata talakawa ganin halin kuncin da jama’a ke ciki.
Duk kokarin da majiyar tamu ta yi na samun jin ta bakin Hon. Gagdi bai yi nasara ba saboda bai amsa sakon kar-ta-kwana ko WhatsApp da aka yi masa ba.