Mon. Mar 31st, 2025

Kwankwaso Tsayayyen Ne Mai Son Ci Gaban Al’umma -Fagge

By Saleh Aliyu Oct 25, 2024

Daga Ibrahim Muhammad Kano.

Shugaban hukumar amintattu na fansho na jihar Kano, Alhaji Habu Muhammad Fagge ya bayyana Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso jagoran Kwankwasiyya da cewa tsayayyen mutum ne mai kishi da son ganin ci gaban al’umma.

Shugaban hukumar amintattun na hukumar fansho na jihar Alhaji Habu Muhammad Fagge ya ce Kwankwaso jagora ne da yake tafiyar da rayuwarsa domin ganin ci gaban al’umma musamman na kasa, gudunmuwa da yake bayarwa tana mutuƙar amfanar al’umma.

Ya ce shekaru 68 da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ya cika a rayuwa al’ummar Jihar Kano shaida ce a kan irin kyakkyawar gudummawa da yake bayarwa ga ci gaban jiha da ma ƙasar nan baki ɗaya daga irin matakai da ya hau kai.

Alhaji Habu Muhammad Fagge ya ce a zamanin da yake Gwamnan jihar Kano a karo na ɗaya da na biyu ya kawo gagarumin sauyi da jihar Kano ta zama abar koyi a tsakanin jihohi domin shi ne ya assasa mayar da barin Kano na zamani abin alfahari ga Kanawa da baki.

Ya ce Kwankwaso jagora ne na bunƙasa ilimi, musamman a tsakanin ‘ya’yan talakawa, shi ne ya samar da jami’o’i guda biyu a jihar Kano da manyan makarantu na koyar da sana’oi guda 25 da tura ɗalibai ƙasashen waje suka yi karatu da dama suka sami ayyuka a muhimman a wurare suna ba da gudunmawa .

Alhaji Habu Muhammad Fagge ya ce suna matuƙar farin ciki da ƙarin shekaru na jagora Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da fatan Allah ya ci gaba da ba shi tsawon rai da lafiya ya ci gaba da ba da gudunmawa domin ci gaban al’umma.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *