
Daga Ibrahim Muhammad Kano
An bayyana jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da cewa jagora ne na fita kunya da ya tasa jihar Kano da ƙasar nan don neman cigaba, Dakta Mani Gwarzo shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo ne ya bayyana hakan.
Ya ƙara da nuna cewa kowa ya ga irin taron mutane a ɗaurin auren ‘yar Kwankwaso da aka yi ya daɗa nuna shi mutumin arziƙi ne, mutumin kirki, sun gode wa Allah da suke bin jagorancinsa, al’umma ta yarda gwarzo ne shi.
Ya ce fatan su a shekara ta 2027 lokacin da za a shiga kakar zaɓe, mutane su gane, makoma ita ce a zo a zaɓi Kwankwaso wanda koyaushe cigaban al’umma ne a gabansa.
Dakta Mani Tsoho shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo ya ce irin yadda ‘yan jam’iyyu mabambanta suka zo Kano don su shaidi ɗaurin auren ‘yar jagoransu Kwankwaso, ya nuna shi mutum ne da yake son cigaban wannan ƙasar ta nuna kowa ya san shi ɗan kishin ƙasa ne.