Daga Hussaini Yero
Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na Funtuwa da kewaye ya kai ziyara ga Majinyata da ke kwance a Asibitin Dandutse da Karamin Asibitin Funtua ya kuma ba Majinyata 70 tallafi kudin dan sayan magani ga kowane su .
Shugaban Kwamitin Busiri Muhammad Kin, ya bayyana cewa, wannan Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na yankin Funtuwa,na daga cikin ayyukan Kwamitin shine tallafawa marasa lafiya da kuma ziyarar Gidan Gyara hali ,inda a bana Kwamitin ya ceto mutane takwas daga gida Gyara hali na garin Funtuwa.kuma ayau gamu cikin wadannan Asibitici na Dandutse da Karamin Asibitin Funtua,munba kowane majinyaci naira dubu biyu kuma Majinyata 70 suka amfana da wannan tallafi ayau daga Kwamitin zagayan gari na Maulidin Annabi (saw) na yankin Funtua .
Anasu Jawabin Kalifan Tijaniya Ali Sa’idu Alti da Malam Aminu Inuwa Zakiru ,sun bayyana cewa,jinya ibadace da Allah ya ke jarabtar bayan sa a koda yaushe hatta Annawan Allah suna gamuwa da jarabawa ta rashin lafiya dan haka zaman jinya da kukeyi ibada ne a wajan Allah.ziyara gareki shima ibada ce wanda Manzan Allah ya umarce mu da muyi dan haka muka kawo maku wannan ziyara da kuma dan tallafi na sayan magani,albarkaci murnar haihuwar Manzan Allah (saw).
Kalifa Ali Sa’idu Alti ya jinjinawa Dahiru Barau Mangal kan ciyarwa da yakeyi a Asibitin ga Majinyata akan haka ne, Kalifa yayi kira ga masu hannu da shuni da suyi koyi da ciyarwa irin ta Dahiru Barau Mangal da taimakon marasa lafiya masu kwance a Asitici.
Kuma Kalifan Tijaniya ya kuma yabawa Malam Asibiti akan yadda suke kula da marasa lafiya da kuma kula da tsaftar Asibitin.
Ansasu jawabin Shugabanin masu kula da Asibitocin,Dr Abdulhadi da Dr Dan Gaye,sun mika godiyar su ga Kwamitin zagayan aka tallafawa marasa lafiya dan yanzu haka akwai majinyantan da basu da kudin sayan magani amma zuwanku ya taimaka masu .akan haka muke godiya a gareku da wannan aiki na alhairi da kukeyi Allah ya taimaki wannan Kwamitin zagayan gari kamar yadda kuka taimaki Majinyatan mu Amin.
Anasa jawabin Shugabanin Karamar Hukumar Funtua,Malam Lawal Sani da ya samu wakilcin,Kamsila Mai kula da lafiya Hon, Mansur Dan Bello ya bayyana godiyar sa ga wannan Kwamitin da fatan sauran Kwamitoci da kungiyiyi zasu koyi da ku wajan taimakon marasa lafiya da kuma wadanda ke zaune a gidan Gyara hali na ceto masu Kannan laifuka.kamar yadda kukeyi.