Wed. Apr 2nd, 2025

Kwamishina Ya Yaba Wa Nasarorin Gwamna Zulum

By Saleh Aliyu Mar 15, 2024

Daga Abdullahi Musa Makka

Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Borno, Honorabul Sugun Mai Mele, ya yaba wa kwazon Gwamna Babagana Umara Zulum da jajircewarsa wajen kawo ci gaba ga al’ummar jihar.

Jihar Borno da ke a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya mai fadin kasa kusan murabba’i kilomita 70,898, an kafa ta ne a ranar 3 ga Fabrairu, 1976.

A tsawon shekarun da suka gabata, shugabanni daban-daban, na soja da na farar hula ne ke mulkin jihar. Sai dai kuma irin sauye-sauyen da ake samu a jihar Borno musamman ta fuskar samar da ababen more rayuwa, ya bai wa ‘yan Nijeriya da dama mamaki.

Mele ya jaddada cewa, a karkashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum, jihar ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar samar da ababen more rayuwa, tallafin rayuwa, bunkasar kudaden shiga na cikin gida (IGR), da inganta harkokin kasuwanci.

“Gwamnatin jihar Borno karkashin Babagana Umara Zulum, ta gina gada biyu, wanda ya zama na farko a yankin Arewa maso Gabas.

“Bugu da kari, an amince da gina gadar sama ta uku a Maiduguri, babban birnin jihar,” Mele ya bayyana.

Ya kuma bayyana nasarar aiwatar da shirin tallafawa rayuwar al’umma da gwamnatin jihar ta bullo da shi, wanda aka dora wa Ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu nauyin kula da shi.

Ya ce wadanda suka ci gajiyar tallafin sun nuna jin dadinsu kan taimakon da aka samu, inda aka gudanar da rabon su cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mele, wanda ke rike da mukamin shugaban kwamitin rabon albarkatun man, ya bayyana cewa shirin na da nufin rage tasirin cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ke yi. An dorawa al’ummar yankin aikin tantance wadanda suka ci gajiyar tallafin bisa la’akari da irin halin da suke ciki na talauci, inda aka ruwaito an Kai wa kimanin gidaje 100,000 hari a fadin kananan hukumomin Maiduguri da Jere.

Wannan rabon yana ɗaya daga cikin ayyukan da gwamnatin Zulum ta yi, in ji shi.

Daga cikin nasarorin da gwamnatin Gwamna Zulum ta samu tun a shekarar 2019 akwai na dawo da layukan wayar tafi-da-gidanka, gyara makarantun da hare-haren Boko Haram ya lalata, sake tsugunar da ‘yan gudun hijira zuwa hedikwatar karamar hukumarsu, gyaran dukkanin manya da kananan asibitoci a kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Bugu da kari, ya samar da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a cikin al’umma, ya dawo da wutar lantarki a Maiduguri, dawo da sarakunan gargajiya zuwa yankunansu, sake kafa hukumomin farar hula a kananan hukumomin da aka kwato, kafa cibiyoyin koyon sana’o’i, gyaran hanyoyi, da shimfida sabbi a Maiduguri da wasu garuruwan.

Mele ya kara da cewa duk da Gwamna Zulum na fuskantar barazana ga rayuwarsa, amma saboda kishina ƙasa da al’ummarsa ya ci gaba da jajircewa wajen ganin ya inganta rayuwar mazauna jihar Borno.

Kwamishina Sugun Mai Mele, wanda ke rike da mukamin kwamishina mafi dadewa a jihar Borno, ya taka muhimmiyar rawa wajen sa ido kan al’amuran kananan hukumomi domin tabbatar da ingantaccen shugabanci ga al’ummar jihar Borno.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *