Daga Ibrahim Muhammad
Tun zuwan gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf aka dawo da karatu a Kwalejin Ilimi ta Ghari da yanzu ta zama Yusuf Maitama Sule College of Education and Advance Studies da ke ƙaramar hukumar Gari da gwamnatin baya ta Ganduje ta rufe da yanzu haka ana gudanar da muhimman ayyuka na gyaran makarantar gaba ɗaya domin kyautata yanayin koyo da koyarwa.
Shugaban Kwalejin Dan Galadiman Farfesa, Abdullahi Asiru ya shaida wa ‘yan jarida haka.
Ya ce suna yi wa gwamnatin Abba godiya domin da farko ma shi ne ya sa hannu aka sauya sunan ƙaramar hukumar daga Ƙunchi zuwa Ghari. Sannan ya sake buɗe makarantar da Kwankwaso ne ya ƙirƙiro ta ake karatun share fagen shiga Jami’a, amma gwamnati da ta gaje shi ta rufe.
Ya ce da Gwamna Abba ya zo ya ce ana so a samar da ƙwararrun malamai da za su koyar a makarantu aka sake buɗe makarantar da ɗaga likkafarta da sauya mata suna ta zama ta ba da shaidar NCE da yin karatun sharar fagen shiga Jami’a da na gyara jarabawa.
Ya ce bayan an buɗe makarantar an yi abubuwa na cigaba domin a da baya da aka gina ta ba katanga, amma ana dawo da ita Gwamna ya sa aka yi mata katanga aka zagaye ta aka yi mata babbar ƙofa ta shiga da fita da ɗakin masu gadi, aka sa jami’an tsaro daban-daban da suke kula da tsaron makarantar, aka kuma samar da malamai ƙwararru guda 91 da hukumar gudanarwa 10
yanzu suna da malamai da ma’aikata 101 da gwamnati ta sahale suke makarantar.
Abdullahi Asiru ya ce yanzu haka ana ta gudanar da aiki a Kwalejin Ilimi na Yusuf Maitama Sule na Ghari babu dare, ba rana, kullum injiniyoyi da ma’aikata a can suka tare ana gyaran ajujuwa, rufi, kujeru, ofisoshin, ɗakunan kwanan ɗalibai da suka lalace lokacin da aka kulle a baya.
Ya ce akwai wuri na koyon sana’a da aka gina a baya na koyon ɗinki da yin sutura da gwamnatin Kwankwaso ta gina a Ghari za su farfaɗo da ita domin koyawa yara sana’a domin su sami ilimi da kuma sana’a na dogaro da kai, kuma akwai rijiyoyin burtsatse huɗu na ruwan daɗi a makarantar da ake gyarawa, yanzu haka hukumar samar da wuta a lantarki a karkara ta Kano an ba su umurni za su sa babban tiransifoma, sannan za a haɗa su da babbar layin samar da wuta na ƙasa, za a kuma sa fitilu masu aiki da hasken rana duk don inganta samar da wutar lantarki a Kwalejin don kyautata tsaro.
Abdullahi Asiru ya ce a baya da aka rufe makarantar an bar ɗalibai ‘yan wucin-gadi da makarantar CAS take kula da su yan aji biyu da ‘yan aji uku, yanzu sun zo sun gaje su za su kai guda 300, yanzu su kuma suna shirin ɗaukar sabbin ɗalibai, sun buga fom guda 3,000 suna ba da da su kyauta ana zuwa daga ƙananan hukumomi 44 ana karɓa kyauta kowane ɗaya a kan Naira 5000 ya kama, amma kyauta suke bayarwa don ba da gudunmuwa ga manufar gwamnati a kan ilimi, kuma suna sa ran za su soma karatu da ɗalibai 1,000. Domin akwai malamai da kayan aiki.
Kuma don kiyaye tsari na addini da al’ada, ɓangaren maza daban, na mata daban. Ba za su yarda a yi zama na haɗaka ba.
Sun kafa doka a kai kowane aji ɓangaren maza daban da na mata, don kiyaye mutunci da darajar da Allah ya yi wa ɗan’adam.
Furofesa Abdullahi Asiru ya ce yanzu haka Kwalejin Ilimin ta Sule Maitama Yusuf ta garin Ghari na da tsangayoyi guda biyar da ɓangaren Ilimi, kimiyya da koyon sana’o’i.
Sannan ƙarƙashin kowanne akwai sassa guda huɗu. Sannan wajen kwanan mata daban na maza daban da cikakken tsaro. Sun kuma ware malamai mata huɗu da za su kula da kare mutuncin ɗalibai mata.
Sannan a ɓangaren maza akwai malamai uku da aka sa su suna kula da maza.
Sanan akwai masallaci da ɗakin cin abinci na ɗalibai da na kallo da wajen motsa jiki da wasanni har ma Kwamishinan Matasa da Wasanni, Mustapha Rabi’u Kwankwaso ya yi alƙawarin samar musu da kayayyakin wasanni na maza da mata.