Daga Ibrahim Muhammad
Ƙungiyar tsaffin ɗalibai na makarantar Firamare ta masallaci ‘yan aji na 88, sun gudanar da taro a karo na farko tun bayan gama makarantar.
Taron da aka gudanar a harabar makarantar ranar Talata, ya samu halartar ɗimbin tsoffin ɗaliban maza da mata da suka zo daga sassa daban-daban a ciki da wajen jihar Kano da wasu daga cikin malamai da suka koyar da su.
Tsoffin ɗaliban ‘yan aji na 88 a taron sun tuna baya da irin rayuwa da suka yi suna ƙananan yara ɗalibai da yadda malamansu suka tafiyar da su da kuma tarbiyyantar da su da har mafi yawansu da suke a raye suka kai matsayin da suka kai.
Su ma wasu daga malaman nasu da suka saura da suka sami halartar taron, sun nuna jin daɗinsu da alfahari da ɗaliban nasu.
Malama Fatima Fagge, ɗaya daga malamai da suka koyar da ɗaliban ta bayyana cewa a lokacin da suke koyar da su sun ɗauke su ne tamkar ‘ya’yansu da ƙanne da suke ba su ilimi da tarbiyya domin su zama nagari masu amfani a cikin al’umma.
Sannan ta ja hankalinsu a kan su waiwayo su kula da tsofaffin malaman nasu da yawanci sun manyanta sosai, kuma suna da buƙatar a riƙa tallafa wa rayuwarsu.
Ƙungiyar tsaffin ɗaliban na makarantar Firamare na masallaci ‘yan aji na 88 a taron sun tallafa wa malamansu da buhunan shinkafa da kuɗin cefane.
Tun da farko shugaban riƙo na ƙungiyar MOPA, Alhaji Abba Kurawa a jawabinsa na maraba ya ce, taron shi ne na farko tun bayan kammala makarantar shekaru 36 da suka gabata.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ta soma ne da sunan MOPA gatan zumunci, sakamakon wasu daga tsoffin ɗaliban da suka haɗa da Umma Madaki da A’isha Wada da Mustapha Musa Soron Ɗinkin suka yi ƙoƙari suka yi gida a kafar sadarwa, wacce ita ta haifar da kafuwar ƙungiyar har Allah ya ba su dama suka shirya wannan taro da gudunmuwar daga ‘yan ajin na 88.
Alhaji Abubakar Abba Kurawa ya bayyana cewa, manufar kafa ƙungiyar ta MOPA shi ne ƙarfafa zumunci da taimakawa juna da makarantar da malamansu suna roƙon Allah ya ba su ƙwarin gwiwa na tabbatar hakan.
Da yake ƙarin haske ga ‘yan jarida, shugaban riƙo na MOPA, Alhaji Abubakar Abba Kurawa ya ce, bayan wasu ɗalibai sun fitar da mahaɗa a manhajar whatsapp sai aka yi shugabanci da zai shirya taro da zumunci da taimakon juna da taimakawa malamai duk da sun nemi taimako a ƙurraren lokaci na haɗa taron, amma ɗalibai sun yi ƙoƙari sosai na tabbatar da taron.
Ya ce an gudanar da taron cikin nasara, an haɗu an ga fuskokin juna da aka daɗe ba a haɗu ba. Wasu ma sun rasu daga cikin su sun yi musu addu’a, an kuma tallafa wa tsofaffin malaman su guda 10 da buhunan shinkafa da kuɗin cefane, su kuma tsofaffin ɗaliban ‘yan’uwansu a wannan haɗuwa da suka yi ne za su gane masu buƙata da za su taimaka musu nan gaba da kuma buƙatun da makarantar ke da su.
Shugaban riƙon ƙungiyar na MOPA, Alhaji Abubakar Ahmad Kurawa ya ce, ya gamsu da yadda aka sami yawan tsofaffin ɗaliban da suka halarta duk da cewa a ranar aiki ne kuma kusan ƙarshen watan na ƙarshen shekara, da ma sun riko Allah kada ya sa su ji kunya, kuma ga shi an yi taro cikin nasara.