Tue. Apr 1st, 2025

Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Ya Kashe Kwarton Matarsa

By Saleh Aliyu Mar 22, 2024

Wata babbar kotu a jihar Ekiti a yankin Ado Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wani matashi mai shekara 28 bisa samun sa da laifin kashe wani mutum da yake zargin yana lalata da matarsa.

Kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito, kotun ta yanke wa Ayodeji Alomoge hukuncin kisa ta hanyar ratayewa bayan ta same shi da laifin kisan kai.

“A ranar 21 ga watan Yuni, 2022, a Ikere Ekiti, Alomoge ya kashe wani da ake kira Ogunleye Ayomide, hakan ya saba wa sashe na 234 na dokar laifuka ta jihar Ekiti, 2021.” in ji Mai Shari’a Jubril Aladejana.

Mahaifin marigayin, Ige Ogunleye, a cikin bayanin da ya yi wa ‘yan sanda, ya ce an yi masa waya cewa dansa (marigayin), Alomoge da abokansa sun yi masa dukan tsiya. “Na garzaya zuwa wurin, na iske dana a cikin wani hali, an ji masa raunuka iri-iri a kansa da bakinsa.

“Na kuma iske Alomoge tare da wasu mutane. Na tambaye shi dalilin daukar matakin da ya dauka, sai ya ce Ayomide ya dade yana hulda da matarsa, kuma ya gargade shi da ya daina, ko kuma ya kashe shi.

“Na dauki Ayomide zuwa wani asibiti da ke kusa, daga baya kuma na kai shi asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin, jihar Kwara, inda daga baya ya rasu,” Ogunleye ya kara da cewa.

Mai gabatar da kara, Kunle-Shina Adeyemo, ya gabatar da shaidu biyar, tare da gabatar da bayanan wanda ake tuhuma, da hotunan marigayin, da kuma rahoton Likita na musabbabin mutuwar a matsayin shaida, kuma kotu ta yi la’akari da su.

Wanda ake tuhumar ya yi magana ne ta bakin lauyansa, Adeyinka Opaleke, inda ya roki kotun da ta yi wa wanda yake karuwa adalci da jin kai, tare da la’akari da abin da ya fusata shi ya dau matakin da ya dauka.

A hukuncin da kotun ta yanke a ranar Alhamis, Mai shari’a Jubril Aladejana ya ce, “Bisa hujjojin da suka bayyana a gare shi, wanda ake kara ya dauki matakin da ya dauka ne sakamakon kishi, kuma bai bi matakan da doka ta tanada ba wajen huce haushinsa.

Saboda haka na sami wanda ake tuhuma da laifin kisan kai da ake yi masa. Don haka aka yanke masa hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Alkalin ya ba da umarnin cewa: “Za a rataye Ayodeji Alomoge a wuyansa har sai ya mutu.”

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *