Wed. Apr 2nd, 2025

Kotu Ta Daure ‘Yan Canji A Kano

By Saleh Aliyu Mar 3, 2024

Daga Hadi Bawa

Mai shari’a Mohammed Nasir Yunusa na babbar kotun tarayya da ke Kano, ya yanke hukunci a ranar Laraba, 28 ga Fabrairu, 2024, wanda ya haifar da hukunci tare da daure wasu mutane uku da ke da hannu a ayyukan canji ba bisa ka’ida ba.

Mutanen ukun da suka hada da Umar Ibrahim Muhammad, Abubakar Yakubu Garba, da Muhammad Tijjani, sun samu kansu a zaman gidan yari na tsawon shekaru uku, sakamakon abin da suka aikata, wanda ya saba wa ka’idojin bayar da lasisi.

Laifukan da ake tuhumar su da aikatawa sun samo asali ne daga yadda suke gudanar da hada-hadar kudaden kasashen waje ba tare da izini ba a cikin Kano, kamar yadda ya bayyana a cikin tuhume-tuhumen da aka yi masu a gaban kotu.

A cewar tuhume-tuhumen, Ibrahim Muhammad an same shi da laifin gudanar da ayyukan canji ba tare da lasisin da ake bukata ba, wanda hakan ya saba wa sashe na 57 (5) na dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na 2020.

Kamar yadda Hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na yanar gizo, waɗanda ake tuhuma sin amince da laifin da ake tuhumarsu da aikatawa, a lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen da ake yi musu a cikin harsunan Ingilishi da Hausa. Wannan amincewa da aikata laifin ya ba da damar lauyan mai shigar da kara, A’isha Tahar Habib, ta roki kotu ta hukunta su, tare da yanke musu hukuncin da ya dace.

A halin da ake ciki, lauyan da ke kare waɗanda ake tuhuma ya nemi a yi musu sassauci a madadin abokan huldar su.

Bisa la’akari da rokon da aka yi masa, mai shari’a Yunusa ya yanke hukuncin, inda ya yanke wa Muhammad, Garba, da Tijjani hukuncin daurin shekara daya a gidan yari. Bugu da kari, an ba su zabin biyan tarar Naira 100,000 (Naira Dubu Dari) kowannensu.

Wannan hukunci ya nuna matsayin kotu kan aiwatar da ka’idoji a fannin hada-hadar kudi da kuma dakile ayyukan haram a cikinsa.

Hukumar EFCC na Kano suka kama su, inda ta tuhume su da aikata hada-hadar kudade ba tare da lasisi ba.

Shigar da karar mutanen da Hukumar EFCC ta yi ya kara jaddada kudurinta da kuma bin ka’idojin da aka tsara a cikin harkar hada-hadar kudi.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *