
Al’ummar jihar Sakkwato na ci gaba da fuskantar kunci saboda tsananin karancin man fetur da ya addabi yankin.
An dai samu cikas a harkokin kasuwanci, inda ’yan kasuwar bayan fage ke sai da man daga Naira 2,000 zuwa 2,500 kan kowace lita, kamar yadda jaridar Neptune Prime ta ruwaito.
Wasu mazauna garin sun yi kira ga gwamnati da ta sa baki don shawo kan lamarin don kada abubuwa su kara tabarbarewa.
Sun ce lamarin ya fara shafar harkokin kasuwanci tare da jawo wa mutane wahala saboda farashin man fetur din a wajen ‘yan bumburutu ya kai Naira 2,500 kan kowace lita.
A halin da ake ciki, Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC Ltd) ya dora alhakin dogayen layukan motocin da ake gani a Legas, Abuja da sauran jihohin tarayyar kasar kan matsalolin kayan aiki da suka samu.
Kamfanin, ya ce an warware matsalolin, kuma nan ba da jimawa ba komai zai koma daidai.
“Kamfanin NNPC Ltd yana son ya fayyace cewa tsananin da aka shiga na karancin man fetur da ake gani a halin yanzu a wasu yankuna a fadin kasar nan ya samo asali ne sakamakon matsalar kayan aiki, kuma tuni an shawo kan su,” in ji sanarwar.
Har ila yau, kamfanin ya nanata cewa har yanzu farashin man fetur bai canza ba.
NNPCPL ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu.