Wed. Apr 2nd, 2025

Jaridar Madubin Arewa Ta Karrama Shugaban Kamfanin HAY Synergy Link

By Saleh Aliyu Mar 31, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Bisa la’akari da irin gudunmuwa da kamfanin Mai Sango Welding and Construction Company, yake wajen koya wa matasa sana’o’in hannu, jaridar Madubin Arewa ta karrama shugaban kamfanin, Alhaji Jazuli Hamza Yahaya da shaidar yabo.

A yayin miƙa shaidar, babban Editan jaridar, Alhaji Ibrahim Nakogari ya ce irin kyakkyawar shaida ta taimako da kyakkyawa da al’umma suka yi masa tasa suka bi diddigi suka tabbatar da hakan shi ya sa hukumar gudanarwa ta jaridar zañe shi ta yi masa wannan karramawa.

Ya ce manufar hakan shi ne don daɗa masa ƙwarin gwiwa da kuma jan hankalin sauran masu sana’o’i yin koyi da shi, sannan ita kuma gwamnati ta lura da irin gudunmawar da yake bayarwa ta riƙa talafawa ƙoƙarin da yake na rage mata nauyin samawa matasa ayyuka na dogaro da kai.

Bayan karɓar shaidar yabon a jawabinsa shugaban kamfanin na Mai Sango, Alhaji Jazuli Hamza Yahaya ya bayyana jin daɗinsa bisa karramawar da jaridar ta yi masa ya ce akwai ɗimbin matasa da suka koyawa aiki suke cin gajiyar lamarin.

Ya ƙara da cewa za su cigaba da ba da gudunmuwa wajen tallafa wa matasa wajen koya musu sana’o’i na hannu don kange su daga zaman banza da ke sa wa su riƙa abubuwa na rashin jin daɗi.

Alhaji Jazuli ya ce za su yi farin ciki idan gwamnati ta Tarayya da ta jiha za ta shiga lamarinsu ta ba su tallafi da za su cigaba da ba da taimako wajen gina matasa a kan sana’o’i domin su zama masu amfani a cikin al’umma.

Jama’a da dama da suka shaidi ba da shaidar karɓar lambar yabon da jaridar Madubin Arewa ta yi wa Alhaji Jazuli, shugaban kamfanin Mai Sangi sun bayyana cewa an yi bisa cancanta da dacewa.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *