Tue. Apr 1st, 2025

Jami’ar FUDMA Ta Yabawa Farfesa Gwarzo Kan Bada Gudummawar Motocin Daukar Marasa Lafiya Guda Biyu, Da Mota Mai Kujeru 60

By Gazali Haruna Jun 30, 2024 #FUDUMA

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) da ke jihar Katsina, ta yaba wa shugaban rukunin Jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa gudummawar motocin daukar marasa lafiya guda biyu da mota kirar ‘Luxurious’ mai daukar mutum 60 da ya bai wa jami’ar.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Ar’mayau Bichi ne ya yi wannan jinjinar a lokacin da ya jagoranci ma’aikatan gudanarwa na Jami’ar a ziyarar godiya da suka kai wa Farfesa Gwarzo a Kano a kwanan nan.

Farfesa Bichi wanda ya bayyana godiyarsa ga Farfesa Gwarzo bisa gagarumin tallafin da yake bai wa FUDMA, ya ce sun kai ziyarar ne da nufin gode wa Farfesa Gwarzo bisa wannan karamcin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa koyo da koyarwa a jami’ar.

Shugaban jami’ar har wala yau ya yaba da irin gudummawa daban-daban na ci gaban jami’ar da Malamin yake ba su wanda ya bayyana shi a matsayin mai taimakon jama’a, inda ya jinjina masa na musamman bisa yadda ya ba su tallafin motocin daukar marasa lafiya guda biyu da kuma motar bas mai daukar mutane 60.

A don haka ya yi kira da a samar da hadin guiwa a tsakanin jami’o’in biyu tare da bayyana kyakkyawan fata cewa wannan zumuncin zai ci gaba da kyautata alakar da ke tsakanin jami’o’in biyu.

A yayin ziyarar godiyar, Farfesa Bichi a madadin hukumar gudanarwa, ma’aikata da kuma daliban jami’ar FUDMA, ya mika wa Farfesa Gwarzo takardar godiya bisa yadda yake ci gaba da bai wa jami’ar tallafi.

A nasa jawabin, Farfesa Gwarzo ya jaddada bukatar da yake akwai na daidaikun mutane su rika yin tasiri mai dorewa tare da tabbatar da an ga irin nasarorin da suka kawo ko da bayan ba su nan.

Ya jaddada kudirinsa na inganta ilimi a Arewacin Nijeriya ta hanyar kara yawan wadanda suka kammala karatu da kuma inganta harkar ilimi.

Farfesa Gwarzo ya kara jaddada bukatar jami’o’i da su mai da hankali kan gina kyakkyawan suna, martaba, tare da kuma gina kyakkyawar kimar ilimi ta yadda za a samu karbuwa da damarmaki a fadin duniya.

Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN wanda ya yi dogon bayani kan dabarun inganta martabar jami’o’i da kuma samar da tallafi domin gudanar da ayyukan bincike, ya bayyana muhimmancin gina suna, tare da kulla alaka da cibiyoyin ilimi na kasa da kasa, da kuma muhimmancin da yake akwai na tasirin kima ga jami’a.

A yayin da yake bayar da shawarar samar da yanayi mai kyau ga masu ilimi domin bunkasa da kuma ba da gudummawa ga ci gaban jami’ar, Farfesa Gwarzo ya jaddada muhimmancin jami’o’i su samar da na su hanyoyin samun nasara, maimakon dogaro da kudaden gwamnati kawai.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *