Fri. Mar 28th, 2025

Izala Ta Sanar Da Sunayen Malaman Da Za Su Gudanar Da Tafsiri A Kano

By Saleh Aliyu Mar 3, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus Sunna reshen jihar Kano, Shaikh Husaini Yakubu Rano, ya bayyana cewa a Azumin bana an tsara yadda tafsirin Alkur’ani zai gudana a wurare daban-daban da da za a yi a faɗin jihar Kano.

Ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a lokacin da aka ƙaddamar da fara tafsirin a masallacin Shahid Shaikh Ja’afar Adam da ke unguwar Tudun Murtala.

Ya ce shi Alƙur’ani abin da ya sa ake karanta shi ake yi wa mutane bayani domin ya shafi dukkan ɓangarori na rayuwa gaba ɗaya ne.

Sheik Husaini Yakubu ya yi nuni da cewa idan aka yi la’akari da yadda aka shiga matsin rayuwa a ƙasar nan, amma daga dukkan alamu yanzu cikin ikon Allah cikin ‘yan kwanaki nan abubuwa sun fara canzawa kayan masarufi na sauƙi.

Ya yi kira ga jama’a su ɗauka idan sauƙi ya zo daga Allah ne, don haka su ma malamai su tsaya su yi wa jama’a bayanai yadda za su koma zuwa ga Allah don samun cikakken zaman lafiya da tsaro a wannan ƙasa tamu.

Shugabanb Majalisar Malamai na ƙungiyar Izala na ƙasa reshen jihar Kano, ya ƙara da yin kira na cewa dukkan inda suke da majalisai da ake gabatar da tafsiri na Alƙur’ani mai girma kada a manta da marayu a tallafa musu.

Ya ce amma irin wannan yanayin idan ya zo musamman a ce ga Sallah ta zo, ko ranar Sallah da ake farin ciki idan yaro ya ga cewa ba shi da kayan da zai sa na Sallah, ga kowa ya fito da nasa, zai tuna cewa da mahaifinsa yana nan shi ma haka zai fito. Sai ka ga a ranar farin ciki, shi kuma ba ya jin daɗi.

Don haka ya ja hankali da tunatar da iyaye da suke a raye su tuna su ma za su mutu su bar nasu ‘ya’yan su zama marayu abin da suka kyautata shi ne zai sa Allah Maɗaukakin Sarki ya ba da masu taimaka musu.

Sannan ya yi kira da kar kuma a manta da masu ƙaramin ƙarfi domin dama daga manufa ta Azumi shi ne masu ƙarfi za su ji wahala da yunwa da ƙishin ruwa yadda talaka yake ji wannan yana sa wa a sami ruhi na taimako, saboda haka yana da muhimmanci a taimaka da abin da Allah ya hore kada mutum ya ce sai ya mallaki wasu abubuwa masu yawa, abin da yake a hannunka ko yaya yake idan dai ka samu dole ka fi wani kai ma ka taimakawa na ƙasa da kai.

Shugaban Majalisar Malaman na ƙungiyar Izala ta jihar Kano, Shaikh Husaini Yakubu Rano.

Ya ce Manzon Allah ya yi umurni a kan tallafa wa na ƙasa da ku, ku kuma sai Allah ya taimaka muku ya tausaya muna fata Allah Maɗaukakin Sarki ya taimaka ya bayar da ikon yin hidima.

An tsara a Azumin bana dai Malamai guda 393 ne za su gabatar da tafsiri a wurare daban-daban na jihar Kano, ciki har da Shaikh Musa Yakub Sautus Sunnah da zai gabatar a mazaunin da Farfesa Abdallah Saleh Pakistan shugaban ƙungiyar Izala na jihar Kano ya saba gabatarwa, wanda a halin yanzu shi ne shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa sakamakon hidindimu na shirye-shirye tafiya aikin Hajji ba zai ba shi dama na zaman gudanar da tafsirin ba a bana.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *