Daga Ibrahim Muhammad
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta samu nasarar kama wasu mutane mata da maza a wani samame da ta kai a unguwannin Ɗanladi Nasudi, Hotoro da Mariri har ma da kan titin Zariya.
Hukumar ta ce a samamen da take yi da ta yi wa suna Kau da Baɗala domin maganin masu ayyukan da suka saɓa da addinin Musulunci da al’alada.
Hukumar ta Hisba ta jihar Kano ta kuma samu nasarar kama wani boka da yake bai wa mata maganin mallakar miji.
Sannan ta yi kira mata su yi wa mazajensu biyayya maimakon bin bokaye.
Mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisba Mujahideen ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema ya ce Hukumar za ta cigaba da samame don kawar da baɗala a jihar Kano.