Mon. Mar 31st, 2025

Hon. Abiola Ya Yaba Da Taimakon Da Alhaji Ɗan’agogo Ya Yi Wa ‘Yan Kasuwa A Kano

By Saleh Aliyu Dec 23, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

An yaba wa Alhaji Lawwali Dan’agogo bisa irin karamci da ya nuna na soma bai wa waɗanda tun farko suke zaune a wajen da aka gina katafaren rukunin kantunana Ɗan’aggo, wani babban ɗan kasuwa a Kano, kuma tsohon kankakin majalisar kansuloli na ƙaramar hukumar Nasarawa, Hon. Sa’idu Uba Ahmad Abiola ne ya yi wannan yabon.

Ya ce babu abin da za su ce da Alhaji Lawwali Ɗan’aggo sai dai addu’ar Allah ya saka masa da alheri, domin ya gina wajen kasuwanci na Ɗan’aggo da kyakkyawan nufi na alheri da taimako. “Domin a lokacin da zai gina ya hana kowa ya zauna bayan ya sayi wajen ya rushe ya gina. Sannan ya ce ya bai wa mutanen da suke a wajen tun ainihi damar su fara zuwa su zaɓi inda za su zauna kafin a bai wa wasu mutane dama,” in ji shi.

Hon. Sa’idu Uba ya ce sai da aka kira masu asalin shaguna a wajen na ainihi suka zaɓa, duk da kuwa ƙannensa da abokan arziƙi sun zo suna buƙatar wurin, amma ya ce a’a, waɗanda ya tarar a wurin sai sun duba sun zaɓa tukunna. “Haka aka yi. Waɗanda ke baya da na tsakiya duk sun dawo gaba. Wannan ya nuna adalci matuƙa,” ya jadadda.

Abiola ya ƙara da cewa adalci na biyu da ya nuna ya zo ya ba da wurin a sassauƙan farashi da ƙananan ‘yan kasuwa da manya za su mallakar rufa wajen. “Sannan ya yi wa wajen tsari na adashin gata, duk wanda yake so ya saya ko kuɗinsa ba su cika ba, ko haya ne ya kama ya kasa kaya, a hankali sai ya cika. In kuma saye ma za ka yi ka zo ka ɗauki wanda ya yi maka ka riƙa bayarwa a hankali. An yi haka ne domin cigaban matasa da kasuwanci na jihar Kano,” ya ce.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *