Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban Hukumar Amintattu na asusun fansho na jihar Kano, Alhaji Habu Muhammad Fagge ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’ummar jihar Kano.
A cikin saƙon nasa, ya bayyana fatan alheri, haɗin kai, da ci gaba yayin da jihar ta fara sabon babi a shekarar 2025.
Ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa da wajen ci gaban jihar Kano.
Shugaban amintattu na hukumar fansho ta jihar Kano ya bayyana ƙoƙarin Gwamnan na bunƙasa ci gaba da magance muhimman buƙatu, inda ya jaddada ƙudirinsa a matsayinsu na shugabanni a Hukumar Fansho na tallafa wa manufofin gwamnatin Abba Kabir Yusuf na biyan kudaɗen fansho da garatuti a kan kari.
Shugaban kwamitin amintattu na fansho na jihar Kano, Alhaji Habu Muhammad Fagge ya ƙarƙare saƙon nasa da yin kira ga al’umma su bai wa gwamnatin Kano haɗin kai da goyon baya domin samar da makoma mai kyau ga jihar.
Ya yi wa kowa fatan alheri da addu’ar ingantar zaman lafiya da bunƙasar arziƙi da nasarar al’ummar Kano da ƙasa baki ɗaya a sabuwar shekarar nan ta 2025.