Mon. Mar 31st, 2025

Gwamnatin Nasarawa ta taya Ma’azu Maifata murnar zama Shugaban ALGON na kasa

By Gazali Haruna Mar 28, 2024 #Nasarawa

Daga Zubairu Lawal

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule yayi kira ga sabon Shugaban Kungiyar Chiyamomi na kasa da ya daukaka darajar jihar Nasarawa a idon yan Najeriya.

Gwamna Abdullahi Sule yace samun wannan Babban Muqami cigabane so sai da ya shafi duk wani Dan jihar Nasarawa.

Yin amfani da kwarewa da nuna dattako da gaskiya adalci da rilon amana zai kara daga darajar al’umman jihar Nasarawa a idon yan Najeriya.

Gwamnan yayi farin ciki da Shugaban Karamar hukumar Lafia Wanda shine Shugaban chiyamomin jihar Nasarawa yanzu an zabeshi a babban matsayi na sabon Shugaban Chiyamomin Nijariya.

Gwamna Abdullahi Sule yayabawa sabon Shugaban Alhaji Aminu Ma’azu Maifata.

Ya kuma rokeshi ya cigaba da nuna dattako da wakilci na gari kamar yadda ya saba ga al’umman jihar Nasarawa.

Sabon Shugaban kungiyar Chiyamomi na kasa Alhaji Aminu Ma’azu Maifata shine Shugaban karamar hukumar Lafia a jihar Nasarawa a ranar Laraba 27/3/2024 aka tabbatar da shi a matsayin Shugaban kungiyar Chiyamomi na tarayyar Najeriya.

Gwamna Abdullahi Sule ya tayashi murna da nuna goyon baya ta bakin Sakataren yada Labaransa Malam Ibrahim Addara cikin wata takardan da ta fito daga gidan Gwamnati a ranar alhamis 28/3/2024.

Al’umman jihar Nasarawa maza da mata sun rika murna da farin ciki ga sabon Shugaba da yimasa adu’ar fatan alheri.

.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *