Wed. Apr 2nd, 2025

Gwamnatin Jigawa Na Ɗaukar Tsauraran Matakai Kan Masu Cin Zarafin Mata da Yara -Batista A’ishatu Jahun

By Saleh Aliyu Dec 17, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Sakatariyar hukumar inganta ayyukan shari’a da gyaran dokoki ta jihar Jigawa, Batista Aishatu Sulaiman Jahun ta bayyana cewa dokar kare haƙƙin yara da aka samar da ita tun 2021 na aiki matuƙa gaya domin tallafawa wanda aka ci zarafin su a jihar Jigawa, musamman a tsakanin mata da ƙananan yara da su ma mazan.

Ta bayyana haka ne da take zantawa da ‘yan jarida a jihar Kano a gefen taro da ta halarta na ƙaddamar da littafi da sabbin shugabannin ƙungiyar lauyoyi mata reshen jihar Kano FIDA.

Ta ce irin ƙorafe-ƙorafe da ake samu a kan cin zarafin mata gwamnati ta dage a kan lallai sai an daƙile matsalar, don haka nema a kasafin kuɗi na bana a jihar Jigawa aka saka N50,000,000 kan ayyukan hana cin zarafi kuma kuɗin an raba su yadda za a maganta lamarin.

Ta ce akwai ƙarin cibiyoyi da za a samar da za a riƙa tallafawa wanda aka ci zarafinsu, wanda a da guda ɗaya ake da shi a jihar Jigawa, yanzu haka ana gina ƙarin guda biyu a ɓangaren Hadejia da kuma ɗaya da zai kula da ɓangaren Ringim da Kazaure, an zuba kuɗi da za a riƙa tallafawa wanda ake cin zarafinsu, ta samar musu kuɗin mota su je cibiyoyin nan a ba su abinci, kuma a tallafa musu da wani abu da suke buƙata.

Babbar sakatariyar Batista A’ishatu Sulaiman Jahun ta ce, yawanci cin zarafi na faruwa ne a kan masu ƙaramin ƙarfi saboda haka ake samar da wani tallafi da za a iya yi musu. Sannan su ma lauyoyyi suna nan suna aiki a hukumar inganta ayyukan shari’a da ma’aikatar shari’a domin ganin an gabatar da laifukan nan yadda ya kamata a kotu da yin shara’unsu cikin ƙanƙanin lokaci.

Ta ƙara da cewa daga shekara mai zuwa idan aka soma shari’a da ta danganci cin zarafi idan aka shigar da shari’ar da yardar Allah ba za a wuce wata shida ba daga lokacin da aka shigar a kotu zuwa lokacin da za a rufe.

“An sa doka mai tsauri da za ta taimaka wajen kawar da cin zarafin mata. Daga cikin hukunce-hukuncen fyaɗe, idan har an sami wanda ya yi fyaɗe yana da cuta mai karya garkuwa jiki, hukumcin kisa ne, idan kuma ba shi da cutar hukuncin ɗaurin shekaru 21 ne a gidan gyaran hali,” in ji ta.

Ta yi nuni da cewa tun daga bara, duk shari’ar da aka yi a jihar Jigawa ta fyade yawanci ana samun su da laifi, domin yadda ake bincike da gudanar da shari’a a laifin fyaɗe ta sauya. “Akwai cibiyoyi da suke taimakawa wajen samar da shaida daga likitoci wanda aka yi wa fyaɗe za a duba a ga me aka samu a jikinta na cuta shi kan shi wanda ya yi fyaɗe shi ma za a duba a gani hakan na taimakawa idan an gabatar da wanda ake zargi a kotu a gane wanda ya aikata laifin,” ta jaddada.

Ta.ja hankalin masu ruwa da tsaki da cewa ya zama wajibi gwamnatoci su haɗa karfi da ƙarfe su jawo ma’aikatu da suka haɗa da na mata na ilimi da masarautu da iyaye da kuma jami’an agaji da na tsaro duk sai an haɗu da su sai a cimma nasara a tare.

Batista Aishatu Sulaiman Jahun Babbar Sakatariyar ta hukumar inganta ayyukan Shari’a da gyaran dokoki ta jihar Jigawa ta yaba da irin gudunmuwa da ƙungiyar mata lauyoyi ta ƙasa FIDA reshen Kano suke yi na ƙoƙarin tallafa wa mata da yara a ɓangaren shari’a.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *