
Hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya, ta bayyana sabon farashin iskar gas a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin da ta samu sa hannun shugaban hukumar NMDPRA, Farouk Ahmed.
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa, sabon farashin iskar gas na kamfanonin samar da wutar lantarki a yanzu ya kai Dala miliyan 2.42 kan kowace lita ta Birtaniya, wanda ya zarce Dala 2 da kobo 18 da ake sayarwa a baya.
Nijeriya na samar da sama da kashi 70 cikin 100 na wutar lantarki daga tashoshin wutar lantarki da iskar gas ne. Don haka karin farashin iskar gas na iya haifar da karin kudin wutar lantarki da zarar hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya ta sake bitar farashin.
Hukumar ta NMDPRA ta kuma kiyasta farashin iskar gas na kasuwanci a kan Dala 2.92, sama da Dalar Amurka 2.5 da ake sayarwa a baya.
A wata sanarwa da Hukumar ƙididdige kuɗin fito ta Nijeriya (NERC) ta fitar a watan Janairun 2024, ta bayyana yiwuwar karin farashin ga kamfanonin rarraba wutar lantarki idan an samu karin farashin iskar gas.
Gwamnati na duba yiwuwar sake nazarin kuɗin wutar lantarki, kasancewar iskar gas babban bangare ne da ake amfani da shi wajen samar da wutar lantarki.
Masu samar da iskar gas da suka hada da kamfanonin mai da iskar gas na kasa da kasa da na cikin gida, sun sha yin kira da a sake yin nazari a kan farashin sa, inda suka jaddada cewa hakan zai zama wani abin karfafa gwiwa wajen bunkasa samar da shi ga masu bukata.
A cikin sanarwar ta ranar Litinin, Ahmed ya ce dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 wadda shugaban kasa ya sa wa hannu a ranar 16 ga Agusta, 2021, ta ba da takamaiman tsari da za a bi wajen kayyade tsarin farashin isar gas a kasuwar cikin gida.