Tue. Apr 1st, 2025

Gwamnan Kano Ya Shawo Kan Matsalolin Rashin Zuwan Mata Makaranta -Hon. Adhama

By Saleh Aliyu Dec 15, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

Babbar mataimakiya ga Gwamnan jihar Kano a kan ilimin ‘ya’ya mata, Hon. Hafsa Aminu Adhama ta ce, tun zuwan gwamnatin Abba Kabir Yusuf, ƙalubalen da suka tarar mafi girma bayan lalacewar makarantu sai yawan yara da ba sa zuwa makaranta, wanda aƙalla ƙiyasi da aka yi a Kano kaɗai yara kusan miliyan ɗaya ba sa zuwa makaranta.

Ta ce wannan ya sa suka tattara hankalinsu gaba ɗaya ganin Gwamna yana ƙoƙarin aikin gyaran makarantu, su kuma masu taimaka masa ƙanana daga ƙasa na ƙoƙarin ganin yaran nan sun kwashe su daga tituna da suke tallace-tallace da kuma wasu maraici ne ya sa ba sa zuwa makaranta, wasu rashin kayan makaranta, wasu kuma tsanani na rayuwa shi ne suke ƙoƙari su kwashe su mai da su makarantu domin su cigaba da karatu.

Ta ƙara da cewa a karon farko sun yi wa yara ‘yan Firamare kusan 2000 a mataki-mataki.

A wannan a karo na biyu na waɗanda za su tafi ƙaramar Sakandire ne ɗalibai mata suka tallafawa na yara 1000 a cikin ƙaramar hukumar Gwale da wasu ƙananan hukumomi.

Hon. Hafsat ta ce a wannan aiki tana da wakilai guda 88 a jihar Kano da suke taya ta aiki kowace ƙaramar hukuma mutum biyu ko tana nan ko ba ta nan kowace ƙaramar hukuma ta san halin ake ciki, amma a wannan karon tana da niyyar daga farkon sabuwar shekarar nan za ta yi tattali da kanta da masu taimaka mata su je su gani da kansu, kuma su riƙa aiki tare.

Hon. Hafsat Amin Adhama ta yaba da irin goyon baya da haɗin kai da take samu daga shugaban ƙaramar hukumar Gwale da sauran ƙungiyoyi bisa haɗin kai da suke ba su, kuma wannan somin ta bi ne, za su cigaba da aiki da ƙungiyoyi da za su game dukkan ƙananan hukumomi na jihar Kano da wannan tallafi ga ɗalibai.

Taron dai ya sami halartar shugaban ƙaramar hukumar Gwale da wasu daga cikin masu riƙe da muƙamai a matakin gwamnatin jihar Kano da ƙaramar hukumar Gwale.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *