Sat. Apr 5th, 2025

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni

By Saleh Aliyu Jan 6, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda bakwai da ya naɗa.

Kwamishinan shari’a na Kano, kuma babban Lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi shi ne ya rantsar da sabbin kwamishinonin, tare da sauran masu bai wa Gwamna shawara.

Har ila yau, Gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin manyan sakatariyar guda shida da aka ɗaga likkafar su zuwa mataki a aikin gwamnati da kuma rantsar da masu ba shi shawara guda 13 daga cikin 15 da aka naɗa.

Tuni dai Gwamnan na jihar Kano ya tura sabbin kwamishinonin zuwa ma’aikatun da aka tanadar musu.

Sabbin kwamishinonin da aka rantsar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince tura su ma’aikatun da za su jagoranta sune kamar haka.

1.Alhaji Shehu Wada Sagagi, da zai kula da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta kano.

2.Kwamared Ibrahim Abdullahi Waya, an tura shi ya kula ma’aikatar da yaɗa labarai ta Kano.

3.Dakta Ɗahir Muhammad Hashim an amince ya riƙe ma’aikatar kula da muhalli ta Kano.

4.Abdulƙadir Abdussalam, Gwamna ya amince ya riƙe ma’aikatar kula da raya karkara ta Kano.

5.Dakta Isma’ila Aliyu Ɗan Maraya, an tura shi ya kula da ma’aikatar kuɗi.

6.Dakta Gaddafi Sani Yakubu, an tura shi ma’aikatar kula da makamashi.

7.Dakta Nura Iro Ma’aji, ma’aikatar ba da kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati.

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin samar da sabbin kwamishinonin ne domin inganta ayyukan gwamnati da Kuma kawo cigaban jihar Kano.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *