Mon. Mar 31st, 2025

Gwamnan Kano Ya Cika Alkawarin Da Ya Ɗauka -‘Yan Fansho

By Saleh Aliyu Jan 11, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Mataimakin na musamman ga Gwamnan jihar Kano a hukumar amintattun na asusun Fansho na jihar Kano. Hon. Ɗalhatu Bichi Ɗan Yallow ya bayyana cewa duk wanda yake kwankwasiyya yake a jam’iyyar NNPP yana kan tsari ne na biyayya.

Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ƙaddanmar da biyan kuɗin garatuti karo na uku da Gwamna jihar Kano ya yi a gidan gwamnati ya ce shi ya sa su a matsayinsu na matasa a tsarin Kwankwasiyya kullum suke ce wa Gwamnan jihar Kano da jagoransu na Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso su gode wa Allah bisa yadda kullum suke dasa ayyukan alheri yara ƙanana da su matasa da suka ɗan tasa har suna riƙe wasu mukamai da wasu damammaki suke koyi da irin kyawawan halaye da suke gani daga gare su a aikace.

Hon. Yallow ya ce a harkar siyasa da suke akwai maƙiya da ba sa son ganin irin cigaba da tsarin Kwankwasiyya ke kawowa al’umma, saboda haka za su iya faɗar duk wani abu da za su ɓata sunan tafiyar Kwankwasiyya sai dai ba za su yi nasara ba, domin ayyukan cigaba da gwamnatin Abba ta Ƙwankwasiyya take a bayyane suke kuma duk wani mai aikata alheri a Kano ɗan Kwankwasiyya ne.

Ya ce biyan kuɗin ‘yan fansho da Gwamnan jihar Kano yake na ɗaya daga alƙawarurruka da ya yi lokacin da ya zaga ƙananan hukumomi 44 yaƙin neman zaɓe ciki har da na biyan ‘yan fansho duba da irin zalunci da ake musu a gwamnatin baya na cire musu kuɗaɗen suna wata da hana su garatuti, idan ma za a ba su sai an bi ta kan wata mata ko ‘ya’ya sun yanki wani kaso daga ciki.

Ya ce amma yanzu Gwamna Abba Kabir Yusuf ya zo yana iya ƙoƙarinsa ya ɗauko shugabanni na kirki masu gaskiya da amana ƙarƙashin Alhaji Habu Muhammad Fagge waɗanda ba su da tunanin yin wani abu da ba daidai ba ya ba su kula da fansho, don haka suna jinjina wa Gwamnan jihar Kano tun zuwanta ya zuba zunzuruntun kuɗi a karon farko ya sa Naira biliyan biyar aka biya ya ƙara zuba shida aka biya su yanzu a karo na uku aka ƙara saka biliyan biyar suka zama biliyan 16 ke nan aka biya ‘yan fansho da a tarihin ƙasar nan ba a taɓa samun Gwamna da ya taɓa saka irin wannan kuɗaɗe ba.

Hon. Ɗalhatu Bichi Ɗan Yalow ya ce da yawa wasu Gwamnoni na tafiya su yi wasu ayyuka saboda wata manufa ko don samun kaso 10 ko don samun wani abu na son kai, amma Gwamna Abba saboda kishi da tausayinsa ga al’umma na ƙasa yake ware kuɗaɗen don biyan masu haƙƙoƙin garatuti ga iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suke a raye domin su yi buƙatun gabansu.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *