Thu. Apr 3rd, 2025

Gwamnan Kano Jinjina Wa Kwamishinan Da Ya Ajiye Aikinsa

By Saleh Aliyu Jan 6, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da ajiye aiki da Injiniya Muhammad Diggol, ya yi a matsayinsa na Kwamishinan ma’aikatar bibiyar aiyuka nan take.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya raba wa manema labarai.

Tun a farkon mulkinsa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Muhammad Diggol a matsayin Kwamishinan sufuri, kafin daga bisani ya sauya masa wajen aiki zuwa ma’aikatar bibiyar ayyuka inda a nan ne ya yi murabus.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Injiniya Diggol bisa ƙoƙari da jajircewarsa da sadaukarwa, da kuma bin ƙa’idojin aiki a lokacin da yake zama ɗan majalisar zartarwa ta jiha.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya yi wa Diggol fatan alheri a harkokin da zai sanya a gaba.

Sanarwar dai ba ta bayyana dalilin ajiye aikin da Diggol ya yi ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *