Mon. Mar 31st, 2025

Gwamnan Kano Alheri Ne Ga Mata -Hadiza Gadanya

By Saleh Aliyu Jan 14, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana gamsuwa da irin ɗimbin gudunmuwa da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ke bayarwa ga bunƙasa cigaban mata ta hanyar ba su kulawa da tallafin dogaro da kai a fannoni da dama da ba su muƙamai masu yawa a ƙunshin gwamnatinsa.

Hajiya Hadiza Gadanya mai bai wa Gwamnan Kano shawara a kan harkokin ƙasa ce ta bayyana hakan a lokacin da take jawabi a taron zuriyar Ibrahim Dabo da aka yi a gidan gwamnati.

Ta ce ba za ta manta ba, a lokacin da za a tura ɗalibai karatu, ta yi wa Gwamna magana tana ganin kamar a cikin mata ba za a sami masu shaidar jarabawar mai daraja ta farko da za a tura waje ba ta nemi a ta sahale a nemi masu daraja ta biyu.

Ta ce sai Gwamna ya ƙarfafe ta da cewa a zaga cikin saƙo da lokunan jihar Kano a nemo mata masu shaidar jarabawar mai daraja ta ɗaya, sai ga shi kuma an samo ɗimbin mata da suke da sakamakon da ba ta yi tsammanin akwai su ba an tura sun tafi karatu wasu sun dawo Gwamna ya ba su aiki a fannoni daban-daban.

Mai bai wa Gwamnan shawara a kan harkokin ƙasa, Hadiza Sani Gadanya ta ce a bisa sahalewar Gwamna Abba Kabir matan Kano suna cikin alheri duk wata ana ba mata ₦50,000 tallafi a dukkan ƙananan hukumomi 44. Sannan a sakamakon ragewa ‘ya’yansu kuɗin manyan makarantu a Kano hakan ya sa ɗalibai da yawa na ta shiga manyan makarantu an ɗauki mata aikin likitoci da kuma lauyoyi.

Ta ƙara da cewa da sahalewar Gwamnan mai ɗakinsa ta tara mata sama da 1000 daga ƙananan hukumomi 44 ta ba su tallafin ₦50,000 kowacce tare da zaƙulo tsofaffi mata ‘yan shekaru 70 zuwa sama 250 aka duba lafiyarsu aka yi musu walima aka ba su atamfofi aka bai wa kowacce ₦250,000.

Gadanya ta yi nuni da cewa a matsayinsu na ‘yan zuriyar Gwamna ana ba su kulawa su ma sosai an kai mata aikin hajji ana ɗaukarsu a ayyuka daban-daban a matakai na jiha da ƙananan hukumomi ba abin da za su yi sai godiya ga Gwamna a madadin matan da ke zuriyar Allah ya saka masa da alheri.

Ta ce taron da aka yi ya zama mai tarihi, dama sun saba ana yi duk shekara kusan shekaru 17 a tara ‘yan’uwa na kusa da na nesa a tattauna abin da yake faruwa da ya shafe su, sai kuma ya zama na wannan karo ya sami bambamci da na baya, saboda ɗaya daga cikin ‘yan zuriyar shi ne Gwamna a jihar Kano, shi ya sa ya ce wannnan taro a karrama shi a zo a yi taron a gidan Gwamna shi ne suka zo aka yi taron cikin farin ciki da annashuwa.

Hajiya Hadiza Sani Gadanya mai bai wa Gwamnan Kano Shawara a kan harkokin ƙasa ta ce ba ta tunanin akwai wata zuriya mai yawan tasu a Kano kuma wannan taro shekara da shekaru ba su taɓa fasawa ba, kuma tana farin ciki cewa Gwamna daga zuriyarsu yake, yana kuma ayyuka na kyautatawa al’ummar Kano da suke yabawa a kai.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *