Mon. Mar 31st, 2025

Gwamna Uba Sani Yana Ba Da Kyakkyawar Kulawa Don Inganta Lafiyar Mata Da Ƙananan Yara -Hon. Ahmad Isma’il Yakawada

By Saleh Aliyu Feb 18, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana Gwamnan jiha Kaduna Sanata Uba Sani da cewa yana bai wa harkar kulawa da lafiyar mata da ƙananan yara muhimmanci.

Shugaban ƙaramar hukumar Giwa Hon. Ahmad Isma’ila Abdullahi Yakawada ne ya bayyana wa ‘yan jarida hakan da yake zantawa da su a tsakar taron sanin makamar aiki da shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kaduna 23 ke gudanarwa a jihar Kano na kwanaki biyar a kan abin da ya shafi harkar lafiya da yadda za su tafiyar da ayyuka domin sauke nauyin
al’umma.

Ya ce wannan na ƙara tabbatar da tsarin da Gwamna Uba Sani ya fito da shi na tallafa wa mata da ƙananan yara a harkar lafiya a faɗin jihar Kaduna.

Ya ce inganta harkar lafiya na daga muhimman ayyuka da Gwamna ya sa a gaba ta yin tsayin daka a kai na tafiyar da dukkan wasu hukumomi don bayar da gudummuwa wajen kula da lafiyar mata da ƙananan yara.

Ya ce, “Dama haƙƙin kula da lafiya na mata da ƙananan yara a matakin farko yana ƙarƙashin ƙananan hukumomi don tafiyar da su wannan na daga dalilin da tasa Gwamnan jihar Kaduna ya sahale suka zo suna taron sanin makamar aiki da ake da tunaninsa da goyon baya da jajircewarsa.”

Shugaban ƙaramar hukumar Giwa, Ahmad Isma’il Abdullahi ya ce, “Mai Girma Gwamna Uba Sani ya nuna abin da ya sa a gaba shi ne inganta harkar lafiya fiye da komai. Yana iya bakin ƙoƙarinsa a kai da ake kuma samun gamsuwa a kai.”

Hon. Ahmad Yakawada ya ce, zuwan sa shugabancin ƙaramar hukumar Giwa sun sami matsaloli iri-iri dama kuma in ka zo shugabanci matsaloli kake fara nema don ka yi maganinsu suna kan ƙoƙarin maganinsu, yanzu haka ma sun warware kusan kashi 70 daga ciki suna sa ran ganin bayan sauran nan ba da jimawa ba da yardar Allah.

Ya yi kira ga al’ummar Giwa su cigaba da ba da goyon baya da yin haƙuri. “Wani abin sai an yi haƙuri, domin wani sai an yi za a ga amfaninsa, amma lokacin da ake yi sai a ga kamar ba shi da amfani. Muna neman goyon baya da haɗin kan al’umma da gudunmuwa na addu’oi da haƙuri in Alah ya yarda za mu yi nasara a kan abubuwa da aka sa a gaba,” ya ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *