Mon. Mar 31st, 2025

Gwamna Abba Kabir ya sami kyakkyawar tarbiyya tun daga gidansu -Muhammad Mashkur

By Saleh Aliyu Jan 14, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cikar shekaru 62 na Gwamna Abba kabir Yusuf a rayuwa da cewa masu albarka ne da ba a taɓa samun Gwamna da ya yi abubuwa na alheri da yawa cikin ɗan gajeren lokaci da hawansa mulki ba kamar sa.

Alhaji Muhammad Hussain Mashkur, ɗaya daga cikin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida a taron da aka yi na zuriyar Malam Ibrahim Dabo da aka yi a gidan gwamnati a ranar Asabar.

Ya ce abin da ya jawo wa Gwamna ɗabi’antuwa da kyawawan hali saboda irin managarciyar tarbiyya da ya samu ne daga iyayensa, musamman mahaifiyarsa irin misalin kyakkyawar tarbiyyarsa ce ta sa ma da ya miƙe zai je ya yi jawabi a taron zuriyar tasu sai da ya je ya gai da mahaifiyarsa a inda take zaune.

Alhaji Muhammad Hussain Mashkur ya ƙara da bayyana cewa ita mahaifiyar Gwamna Abba Kabir Hajiya Naja’atu mutuniyar kirki ce, wacce ta koyar da shi tarbiyya ta sanin kima da girmama mutane da tausaya musu. Don haka rayuwarsa take cike da albarka.

Ya ce irin kariyar Ubangiji da Gwamna Abba Kabir yake samu daga makirci da mahassada da makiya suke shirya masa sakamakon irin tausayawa da yakewa na ƙasa ne da son yara.

Muhammad Hussain ya yi nuni da cewa tun kafa ƙungiyar ake taron a gidan marigayi Ɗan Makwayo har yanzu da Allah ya kawo Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamna ba a taɓa yin taron kwatankwacin na wannan karon ba da aka yi a gidan gwamnati.

A ƙarshe Alhaji Muhammad Husaini Mashkur ya yi kira ga ‘yan’uwa da abokan arziƙi a kan su dage wajen ci gaba da yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf fatan alheri da addu’oi a kan Allah ya yi riƙo da hannayensa ya gama zangon mulkinsa lafiya. Su kuma al’ummar jihar Kano gaba ɗaya su alkinta ƙuri’unsu zaɓe mai zuwa su sake ba shi goyon baya domin cigaba da ayyuka da yake na bunƙasa cigaban jihar Kano da al’ummarta.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *