Daga Ibrahim Muhammad
A cigaba da ayyukan tallafawa cigaban al’umma da Gidauniyar TAMALAM ƙarƙashin jagorancin Injiniya Dakta Saleh Musa Wailare take a fannoni daban-daban musamman a ƙananan hukumomin Ɗanbatta da Makoɗa.
A wannan karon ma kamar yadda ta saba ta kai ziyara gidan masu fama da larurar ƙwaƙwalwa na Ɗanbatta da ake kira da Ɗanbatta Rehabilitation Centre.
An yi wa musu larurara gyaran muhalli da suke zaune da aski da yankan farata.
Gidauniyar ta TAMALAN ƙarƙashin jagorancin Injiniya Dakta Saleh Musa Wailare kamar yadda ta saba a ranar Sallah, kuma za ta kai abincin Sallah gidan gajiiyayyun da kayan sawa na Sallah. Sannan kuma za a ba su sabulai na wanka da na wanki, tare da mazubin ruwa da na abinci domin amfanin yau da kullum.