Fri. Mar 28th, 2025

Gidauniyar Ɗangote Ta Ƙaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya

By Saleh Aliyu Mar 17, 2025

Gidauniyar Aliko Ɗangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, wanda aka ƙaddamar a ranar Alhamis, ta ware kuɗi kimanin Naira Biliyan16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu naƙasa da kuma marasa ƙarfi.

Sama da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo gram 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Ɗangote.

Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, shugaban gidauniyar, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne mai nauyin kilo gram 10, ga ‘yan Nijeriya marasa ƙarfi da raunana, a ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan, kamar yadda yake a tsarin kamfani da kuma gidauniyarsa na nuna jinƙai ga ‘yan ƙasar.

Ɗangote, wanda ya samu wakilcin ‘yarsa, Hajiya Mariya Aliko Ɗangote, ya ce: “Shirin na wannan shekara, an yi shi ne da nufin nuna tausayi da jinƙai da nuna kulawa wajen taimakon jama’a bisa la’akari da halin da ake ciki na matsin rayuwa da durƙushewar tattalin arziƙi.”

Ya ce gidauniyar ta fara ƙaddamar da rabon tallafin ne a jihar Kano, bayan nan za a ci gaba da rabawa zuwa sauran jihohi, domin tabbatar da ganin cewa abincin ya isa hannun waɗanda aka yi domin su a ɗaukacin ƙananan hukumomin Nijeriya.

Alhaji Ɗangote, hamshaƙin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun haɗa kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabuƙata a kowace jiha da ke faɗin Nijeriya.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci ƙaddamar da rabon tallafin abincin a matakin ƙasa na wannan shekara, ya ce, aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinƙai da kulawar Alhaji Aliko Ɗangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya.

Gwamnan, wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a ɗaukacin ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar Kano.

A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar Jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko Ɗangote, Zouera Youssoufou ta ce an tsara shirin ne a matsayin wata hanya ta tallafa wa gwamnatoci wajen yaƙi da talauci da yunwa a Nijeriya.

Muƙaddashin Babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Dr. Mujahid Aminudden ya gode wa gidauniyar ta Ɗangote kan bijiro da wannan shiri, inda ya roƙi sauran ‘yan Nijeriya da su yi koyi da halin Ɗangote.

Ya ce Hukumar Hisbah za ta tsaya tsayin daka wajen ganin tallafin ya je hannun waɗanda suka cancanta.

Wani da ya yi magana a madadin waɗanda suka ci gajiyar tallafin mai suna Ibrahim Ahmed ya yaba wa Aliko Ɗangote, inda ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da taimakonsa a harkokinsa na kasuwanci.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *