Tue. Apr 1st, 2025

EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Mata 4 Bisa Zargin Kawo Cikas A Shari’a

By Saleh Aliyu May 2, 2024

Daga Hadi Bawa

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta gurfanar da wasu mata hudu a gaban mai shari’a A.A Bello bisa zargin kawo wa aikinsu cikas.

An tsare su ne bisa zargin hana jami’an EFCC yin aiki bisa doka da kuma cin zarafin jami’an Hukumar.

Wadanda ake zargin sune: Rukayya Ahmed Mustapha, Sadiya Usman Mohammed, Ameera Uthman da Nafisat Usman.

An gurfanar da su a gaban kuliya bisa tuhume-tuhume daban-daban da suka shafi hana ayyukan da doka ta tsara .

Da ake karanta masu tuhumar da ake masu Sadiya Usman Mohammed: “Ke Sadiya Usman Mohammed a ranar 15 ga Afrilu, 2024 a Kaduna, da ke aiki a babbar kotun jihar Kaduna da gangan kin hana jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) aikin da doka ta ba su dama.

“A yayin da Hukumar EFCC ke gudanar da wani aiki bisa doka a gida mai Lamba 13 Jafar Organizer Street, Rigachukun, Kaduna, wanda ya aikata laifin da ya saba wa sashe na 38 (2) (a) na dokar hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.”

“Dukkan wadanda ake zargin sun ki amsa laifin da ake tuhumarsu da shi a lokacin da aka karanta musu, lamarin da ya sa lauya mai gabatar da kara, K.S Ogunlade ya roki kotun a tsare waɗanda ake tuhuma din kafin su gabatar da shaidu.

Mai shari’a Bello, bayan ya saurari dukkanin lauyoyin bangarorin biyu ya buƙaci a mika waɗanda ake tuhuma din gidan yari na Kaduna, sai dai Sadiya Usman Mohammed, wacce take shayarwa za a ci gaba da tsare ta a hannun EFCC.

Alkaline ya dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga Mayu, 2024 don sauraron bukatar neman belinsu.

An kama wadanda ake zargin ne da laifin kawo cikas, tare da hana jami’an hukumar EFCC na Kaduna gudunar da aikinsu a lokacin da suke kokarin cafke wata Hadiza Usman, wacce ta ki bayyana a gaban kuliya bayan an ba da belinta.

A yayin da ake kokarin kama su, wadanda ake zargin hudu sun fito fili sun far wa uku daga cikin jami’an Hukumar, sannan suka ciji wani ma’aikacin EFCC din.

Duk da rigimar da wadanda ake zargin suka yi, jami’an sun ci gaba da da’a da sanin makamar aiki, ba su yi kasa a gwiwa ba, suka kama wadanda ake zargin ba tare da wani tashin hankali ba.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *