Daga Ibrahim Muhammad
Babban mai taimaka wa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf a kan harkokin ɗalibai, Hon. Ibrahim Ma’aji Sumaila, ya bayyana cewa harkokin cigaban ilimi a jihar Kano kwalliya tana biyan kuɗin sabulu a ƙasa da shekaru biyu da zuwan gwamnatinsu.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin ƙaddamar da tallafin kaya ga ‘yan makaranta karo na biyu da mai taimaka wa Gwamna a kan ɗalibai mata, Hon. Hafsat Amin Adhama ta gudanar a karo na biyu da aka yi a ɗakin taro.
Ya ce kowa ya san irin yanayin da Gwamna ya zo ya tarar da harkar ilimi da kuma yadda ake a yanzu ko babu komai daga kan malaman makaranta an kyautata albashinsu an daina yi musu yanke-yanke ana sakin albashi a kan lokaci wanda a baya sai a yi kwana 40 ba su samu ba.
Ya ce sannan makarantu an same su a lalace, wasu babu rufi ba allo ba komai, sun zama kamar kango, Gwamna ya ba da aiki ta ƙarƙashin CRC ana gyara su, aka ba da kwangila gyarawa da gina sabbin ajujuuwa, bayan sanya kaso mafi yawa a kasafin kuɗi a shekararsa ta farko kashi 99.9.
Sannan a wannan shekarar ya ƙara yawan kasafin ya koma kashi 31.
Sannan kafin nan dama ya ƙaddamar da dokar ta ɓaci a kan ilimi, domin a farfaɗo da harkar da nufin maganta yanayi da ya tarar da shi
Hon. Ibrahim Ma’aji Sumaila ya yaba da irin wannan tallafi da mai taimaka wa Gwamna Hon. Hafsat Amin Adhama a kan harkar ɗalibai mata ƙanana take, wacce ita ma tana daga wanda ta ci gajiyar wannan tsari na taimakon ilimi a lokacin da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yana kan mulki, yanzu ita ma damar da ta samu a hannunta ta ya kamata ta taimaki na ƙasa, musamman marasa ƙarfi.
Ya ce dama shi irin wannan aiki ya wuce a zura wa gwamnati ido ita kaɗai ya kamata a ce an sami mutane da za su zo su saka hannu a taimaka domin al’umma suna da yawa a jihar Kano, kuma ga ɓarna da aka zo aka tarar an yi wa harkar ilimin da yawa domin ɓarna a rana ɗaya tana iya yiwuwa, amma gyara ba zai yiwu a rana guda ba.
Ya ƙara da cewa jihar Kano tana buƙatar mutane irin su Hafsah Adhama domin su cigaba da ba da gudunmuwa ta zaƙulo mutane ɗaiɗaiku daga kanne da maƙwabta ko daga ƙananan hukumomi domin su taimake su a kan ilimi, domin idan ba a yi irin wannan taimakon ba karatun sai ya ƙi yiwuwa saboda yanzu ana wani yanayi da kowa ta abinci yake ga kuma yawan al’umma.
Hon. Ibrahim Ma’aji Sumaila ya ce, “Yanzu saboda irin kulawa da sauƙaƙawa a harkar ilimi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bijiro da shi a yanzu karatu ya fi sauƙi da araha a jihar Kano a dukkan faɗin ƙasar nan, domin ana digiri a N15,000. Ana NCE a ƙasa da N10,000. Duk ƙasar nan ba inda aka samu irin wannan garaɓasa irin jihar Kano,” in ji shi.