Fri. Mar 28th, 2025

Darakta-Janar Na Yaɗa Labaran Gwamnan Kano Sanusi Bature Ya Yaba Wa Sarkin Kano

By Saleh Aliyu Mar 4, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Darakta-janar na yaɗa labaran Gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ziyarci ofishin ‘yan jaridar fadar Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll, tare da yabawa da irin cigaba da aka samar.

Ya Jinjina wa Mai Martaba Sarkin Kano bisa yadda ya ga ofishin ‘yan jaridar cike da kayan aiki na zamani da masarautar Kano ta samar don kyautata ayyukan wakilan jaridun fadar.

A nasa jawabin, shugaban ‘yan jarida na fadar Sarkin Kano, Saddam Nasir Na’ando ya gode wa Darakta janar ɗin na yaɗa labarai na Gwamnan jihar Kano, bisa ziyarar sannan da ba shi tabbacin fitar da sahihan labarai don amfanin al’ummar.

Ya ƙara da gode wa fadar Sarkin wajen samar da sabbin kayan aiki na zamani da aka yi don inganta da kyautata ayyukanasu.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *