Daga Hussaini Yero, Funtua

Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta karbar lambar yabo karo na biyu daga kungiyar Peace Ambassadors Network ta Najeriya.sakamakon fice wajan kulawa da Walwalar Mata Da Marayu.
Hajiya Huriyya ta karbi lambar yabon a wurin taron ya gudana a cibiyar kungiyar samar da zaman lafiya da magance rikice-rikice da ke Abuja.
Mataimakiya ta musamman akan yada labarai ta Matar Gwamna,Zahara’u Musa ce ta bayyana haka a takardar da ta sa mahañnu ga manema labarai a Gusau.
Acewar ta ,Jim kadan bayan karbar lambar yabon, Uwargidan Gwamnan, Huriyya Lawal, ta bayyana godiyar ta ga Allah Madaukakin Sarki da kuma wadanda suka shirya taron da suka karrama ta a cikin wasu fitattun ‘yan Najeriya masu matukar daraja da kima.
“Na yi farin ciki da Jindadi matuka bisa girmama ni da ku kayi da kuma kasancewa cikin wadanda suka ci gajiyar wadannan kyaututtuka.
Zaɓata cikin waɗanda aka ba wannan Lambar karramawa a matsayi mace Mafi tsayuwa ga lamurran mata kan sha’anin daidaiton jinsi abun jinjina ne da godiya Matuka.
“Na gode muku kwarai da gaske da kuka amince da irin gudunmurwar da muke bayarwa Kan Sha’anin mata da Yara.
Duk da haka, ta ba da tabbacin ci gaba da ƙaddamar da shirye-shiryen ƙarfafawa Al’umma waɗanda ke da tasiri kai tsaye izuwa gare su.
Hajiya Huriyya Lawal ta kuma bayyana mijinta Dauda Lawal a matsayin Jigo da ma’aunin dukkan nasarorin da ta samu.
A karshe Hajiya Huriya Dauda ta sadaukar da kyautar karramawar ga Al’ummar jihar Zamfara baki daya.