Daga Ibrahim Muhammad
Shugaban kamfanin taki na Rara Agrovet, MD. Alhaji Abdullahi Rara ya bayyana cewa harkar noma yana tafiya daidai a jihar Jigawa sakamakon gwamnati ta na bakin ƙoƙarinta sannan kamfanoni na waje na gida irin nasu sun shigo suna taimaka wa manoma.
Ya ce kusan kowane gari a lungu da saƙo na cikin jihar babu inda ba sa ba su tallafi da taimako na taki idan sun gama noma su biya a ko’ina sun shiga suna taimaka wa manoma ba domin manoma suna samun irin wannan taimakon daga gare su ba, da wahalar da za a shiga da ƙarancin taki da sai ya ci musu tuwo a ƙwarya.
Ya yi nuni da cewa a ɓangaren gwamnati ana samun matsala na idan ta bai wa manoma tallafi na rancen kayan noma, amma a ƙi dawo da shi, an yi shiri na ƙungiyoyin manoma da tsare-tsare daban-daban na gwamnati, amma ba su ɗore ba sakamakon ba a dawowa da bashin da ake ba su.
Amma ya ce su a nasu tsarin na kamfanoni na cikin gida da suke taimakon manoma a jihar Jigawa suna da tsare-tsare da gwamnati ba su da shi, su sun tsara da lauyoyin su da sauran duk wani mai ruwa da tsaki sun tsara abin da zai tafi daidai sun zauna da su, kuma komai yana tafiya yadda ya kamata ba su fiya samun matsaloli ba.
MD. Alhaji Abdullahi Rara ya ce ita gwamnati a tsare-tsaren ta ba ta neman kamfanoni, ƙalubalen da take samu na rashin neman kamfanoni ne a ciki da za ta nemi kamfanoni su shigo da su za su sami nasara wajen tsara yadda za a tallafa wa manoma sauƙin samun taki da yadda za su biya, amma sai gwamnatin suna yin abin ne da ka shi ya sa abin da ake bai wa manoma ba ya dawowa.