Mon. Mar 31st, 2025

Cibiyarmu Ta Manaru AlHuda Za Ta Ciyar Da Masu Azumin -Kulliya Fatima Muhammad Fagge

By Saleh Aliyu Feb 22, 2025

Daga Ibrahim Muhammad

Cibiyar Manarul Alhuda da ke a jihar Kano a bana ma sun tsara shirye-shirye na faɗakarwa na tsawon mako bakwai a cikin watan Azumin Ramadan.

Mai kula da makarantun Amiratul Kulliya Malama Fatima Muhammad Fagge ta bayyana hakan.

Ta ce yanzu haka sun shiga mako na biyu ma da soma wa’azozzuka da suka saba duk shekara da ake ƙarƙashin jagorancin shugaban Cibiyar ta Manarul AlHuda babban Shehun Malami Umar Sani Fagge da ake gabatar da maudu’i na littafin Ishiriniya, wanda yabo ne na Manzon Allah da aka gada iyaye da kakanni.

Ta ce idan aka yi la’akari da tasirin Ishiriniya da yadda mawaƙa suke fitowa suke yi ya zama wajibi a fassara shi domin ta zama mamuniya ga masu sakin baki ga shugaba Manzo (SAW) su ga yadda waɗanda suka san sirrin abin suka lanƙwasa harshe Allah ya riƙe, sama da ɗaruruwan shekaru bai ɓata ba. “Duk wanda ya san Ishiriniya ya san akwai sirri a cikinta,” in ji ta.

Malama Fatima Muhammad Fagge ta ce don haka naza da mata aka fito da wannan lakca don su gane cewa ba a yabon Annabi don neman kuɗi, kuma sai da ilimi ake yin yabo. “Wannan ya sa yau shekara ta uku ke nan a Cibiyar tasu ake karantar da fassarar Ishiriniya da hakan tasa ake cimma nasarori,” ta jaddada.

Ta ƙara da cewa akwai malamai daban-daban mabambanta da suke shigowa suna lakca irin su Malam Nur Arzai, Dakta Bashir Muhammad Fagge, Mu’azzam Mai Bushira, Dakta Dukawa suna faɗakarwa.

“Sannan ana nusar da mata sirrin da amfanin tsirrai da ke kewaye da su a gida yake. Yadda za su yi amfani da su wajen magunguna. Misali ka ce wanda ya haɗa tafasa ko zogale ko rama ko dinkin. Ko ka ɗauko zuma. Duk irin wadannan cima da ke kewaye da ƙasar Hausa da irin tasirinsu ana samun nasarar nuna musu muhimmancinsu,” ta bayyana.

Ta ce a bana ma akwai tsari na ciyarwa da za su yi kamar yadda suka saba na adadin kwanakin watan Azumi da ranar Sallah don mutane da suke da rauni ba su da inda za su je su ci abinci na buɗa baki ko su ci abinci ranar Sallah. Kullum a kan cinyar da mutane kama daga 300 zuwa ƙasa ko sama da haka. A bara sun iya ciyar da mutane sama da 10,000,” in ji ta.

Malama Fatima Muhammad Fagge ta ce ban da waɗanda suke zuwa sauraron lakcar daga ƙananan hukumomin birni har daga arewaci da kudancin ƙananan hukumomi ake zuwa a haɗu tamkar ‘yan’uwa. Sannan taron na kyautata tsarin zamantakewar mata a gidajen mazajensu.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *