Daga Ibrahim Muhammad
An ɗora alhakin kashe harkar kasuwanci da noma a ƙasar nan a kan tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, musamman a Arewa da yanzu sai dai abin da ba za a rasa ba, domin kafin zuwan sa ₦3000 ake sayen buhun taki, yanzu sai an saya sama da N40,000.
Wani fitaccen manomi, kuma ɗan kasuwa, kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kano, Alhaji Nasiru Agalawa Kafin Agur ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida
Ya ce kafin zuwan Buhari kwantena za ta zo daga ƙasar waje in ka yi oda a miliyan bakwai zuwa 10, amma tunda Buhari ya zo kwantena ɗaya ana maganar sama Naira miliyan 90 ne. Mota ƙirar Gollf kuwa ba ta wuce N380,000 ba, amma yanzu Naira miliyan shida saboda Buhari ya lalata harkar kasuwanci.
Alhaji Nasiru Agalawa ya shawarci al’ummar ƙasar nan abin da ya rage musu su dage da yin addu’o’in Allah ya sassauta mana, ya kawo shugabanni nagari. Sannan kuma a natsu a zaɓe mai zuwa na 2027 a kau da son rai su zaɓi wanda zai taimaki ƙasar nan. “Kada mutane su karaya, ko su gajiya su ƙi fitowa yin zaɓe a gaba. Hakan shi zai ba da dama azzalumai su ci gaba da mulki. A fito a zaɓi wanda ya fi cancanta,” in ji shi.
Alhaji Nasiru Agalawa ya ce a matsayinsa na ɗan jam’iyyar PDP da ba ta da ko da kujerar Kansila a jihar Kano, shi dama ba gwamnati yake bi ba, yana tsaye ne a kan ƙafarsa. Kuma al’ummar ƙasar nan shaida ne talakawan Nijeriya sun ji daɗi a gwamnatin PDP da ta gabata, “Domin a lokacin ne idan mutum ya zo wajenka da buƙatarsa na zai sai mota ne ko zai gyara gida ko wani abu, amma yanzu da ya zo maka sai ka ji ya ce ko na garin kwaki ne a taimaka masa saboda APC ta lalata ƙasa,” ya bayyana.
Don haka ya ce al’ummar Nijeriya a 2027 a tsaya a zaɓi wanda ya dace, kuma suna da kyakkyawan zaton Wazirin Adamawa Atiku Abubakar zai sake fitowa takara, kuma kowa ya san shi ba ɓarawo ba ne, yanzu ma shi kaɗai ya rage yake gaya wa gwamnatin tarayya ta APC gaskiya. Idan aka kyautata zai ce an yi daidai. “In Allah yarda zai sami mulkin ƙasar nan ya farfaɗo da noma da kasuwanci da tattalin arzikin ƙasa,” in ji shi.
Alhaji Nasiru Agalawa ya bayyana cewa a matsayinsa na ɗan jam’iyyar PDP a jihar Kano bai san da cewa an yi zaɓe na shugabannin jam’iyyar ba. “Idan an ce an yi zaɓe ina ne ofishin shugabanta? Sai dai nan gaba jam’iyyar za ta samar da halastaccen shugabanci a kowa ne mataki,” ya ƙarƙare.