Mon. Mar 31st, 2025

Bankin NEXIM Na Da Kyakkyawar Alaƙa Da ‘Yan Kasuwa -Tajuddeen Yakub

By Saleh Aliyu Dec 30, 2024

Mataimakin shugaban reshen bankin NEXIN na jihar Kano, Tajuddeen Yakub ya bayyana farin cikinsa bisa karamawar da majalisar bunƙasa ƙananan masana’antu da sana’o’i Kano Council of Traders And Entrepreneurs (KASCOTE) suka yi musu a yayin taron bita da suka shirya wa ƙungiyoyin manoma da masu ƙananan masana’antu a kan bunƙasa harkokinsu.

Ya yi nuni da cewa, “In ka yi abu na kirki aka karrama ka abin alfahari ne cewa wani ya ga abin da kake ya karrama ka abin alfahari ne,” in ji shi.

Tajuddeen Yakub ya ce wannan ya daɗa ƙarfafa musu gwiwa, sannan a wajensu abin da suke kamar somin taɓi ne a kan abubuwa da za su ƙara yi kamar yadda aka kula aka san suna yi za su zage damtse a kai.

Tajuddeen Yakub ya ce suna da kyakkyawar dangantaka da ‘yan kasuwa mutuƙa shi ne ma ya sa suka sami wannan karamci da har wannan majalisa ta ‘yan kasuwa KASCOTE ta karrama su.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *