Tue. Apr 1st, 2025

Bai Dace Ba Al’umma Ta Riƙa Lalata Kayan Gwamnati -Dakta Ƙofar

By Saleh Aliyu Dec 28, 2024

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana cewa gwamnati tana kawo abubuwa na ci gaba a ko’ina, amma al’umma ne suke lalata su, hatta tituna ma fasawa ake, wuta da ruwa ba a biya, “Ba ma irin mu Hausawa da ba mu da aiki, illa mu ga cewa duk namu da ya ci gaba, an riga an kada shi an jawo shi ƙasa”.

Dakta Yakub Adam Ƙofar Mata, babban sakatare a ma’aikatar taimako da rage talauci na ƙasa ne ya bayyana hakan da yake zantawa da manema labarai a taron tsofaffin ɗalibai na makarantar Firamare ta Ƙofar Nassarawa.

Ya kara da cewa, “Duk da haka kuma ba za mu ce kar a yi abin da ya kamata ba, wanda yake da hali ya je ya taimaka wa makarantarsu, ko ya taimaka wa mutanen unguwarsu dukkanninmu, gaba ɗaya mu tashi tsaye mu tabbatar mun yi wannan. Muna fatan Allah ya taimaka mana kan haka”.

Ya yi nuni da cewa duk wani mataki da mutum ya zama a rayuwa ya tuna baya, domin ita ce asalinss,. “Idan ba ka da tushe mai kyau ba ma irin na makarantar Firamare, domin ko ka je Jami’a ma, babu wani tushe ingantacce da ya fi na makarantar da ka soma,” in ji shi.

Dakta Kofar Mata,
ya ce, makarantarsu ta Ƙofar Nasarawa da suka yi a matsayinsu na tsofaffin ɗalibai a nan suka tashi, Allah kuma ya taimake su suka yi karatu da samun ingantaccen karatu. “Wannan taro da muke, rana ce ta farin ciki da suke gode wa Allah da muka zo muka ga tsohuwar makarantarmu muka haɗu da tsaffin abokai da ‘yan’uwa,” ya tabbatar.

Ya ce, “Ya kamata duk ɗa na gari ya jiƙan na baya. Dama ce, idan Allah ya ba ka, ka yi amfani da ita. Duk tsoffin ɗaliba ya yi wa makarantarsa abin da ya dace don a sami ci gaba,” ya ƙarƙare.

Related Post

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *